An kama babban jami’in shige da fice da manyan bindigogi a Abuja

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Jami’an ’yan sanda da suke ofishin Babban Birnin Tarayya Abuja sun cafke wani babban jami’in Hukumar Kula da Shige da Fice ta Nijeriya (NIS) ɗauke da manyan bindigogi da harsasai daban-daban.

An ruwaito cewa, wanda ake zargin, wanda har yanzu ba a bayyana sunansa ba, an kama shi ne a unguwar Zuma a yammacin ranar Litinin.

An tattaro cewa jami’in da ya kasa yin cikakken bayani kan yadda ya samu makaman da kuma inda zai kai su, ana zarginsa da yiwuwar cinikin makamai ga masu aikata laifuka.

A cewar majiyoyi, kama shi ya biyo bayan rahoton sirri da aka samu daga masu ba da rahoton sirri.

An gano cewa makaman da aka ƙwato daga hannunsa sun haɗa da manyan bindigogi.

“Mun ƙwato gidan harsasan AK-47 guda huɗu; gidan harsasai guda huɗu na bindigar CZ Scorpion; Bindigogin CZ Scorpion guda biyu, alburusai maau tsawon 139 da kuma bindigogin Diakon da CZ guda biyu,” inji wata majiya.

Kwamishinan ‘yan sanda na babban birnin tarayya Abuja, CP Olatunji Disu ya tabbatar da kama wanda ake zargin.

Ya ce ana yi wa wanda ake zargin tambayoyi, inda ya ce za a yi karin bayani daga baya.

“Dazun nan ne suka kawo min wanda ake zargin ana yi masa tambayoyi. Wannan shi ne abin da zan iya tabbatarwa a yanzu,” inji shi.