Ban gaza wajen goyon bayan Tinubu a 2023 ba – El-Rufai

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, a ranar Litinin ɗin da ta gabata, ya yi watsi da iƙirarin cewa, ya gaza goyon bayan Shugaba Bola Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na 2023, inda ya bayyana cewa bai ɗauki irin waɗannan zarge-zarge da zafi ba.

Tinubu da ke samun goyon bayan jam’iyyar APC, ya lashe zaɓen ne da manyan ‘yan takarar adawa – Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP da Peter Obi na jam’iyyar Labour.

El-Rufai, jigo a jam’iyyar APC, ya kasance a tsakiyar tattaunawar siyasa, inda ya bayyana cewa ra’ayinsa kan mulki ba zai canja ba, ba tare da la’akari da irin rawar da ya taka a gwamnatin Tinubu ba.

A ‘yan kwanakinnan dai ana ta samun cece-kuce tsakanin tsohon gwamnan Kaduna Ei-Rufai da ‘ya’yan jam’iyya mai mulki na APC da kuma rashin jituwa da ake zargin akwai tsakaninsa da gwamnan jihar na yanzu Uba Sani.

A ranar Lahadin da ta gabata, wani mai amfani da ɗ, Yusuf Tukur, wanda ya wallafa a shafinsa na Tiwita matsayin #realYusufTukur, ya yi ikirarin cewa Tinubu da abokansa sun nemi goyon bayan El-Rufai kafin zaɓen amma daga baya suka zarge shi da ƙin mara musu baya.

Da yake mayar da martani, El-Rufai ya bayyana ta shafinsa na Tiwita cewa ba shi da wani buri na ƙashin kansa daga ayyukansa na siyasa, ya aara da cewa abubuwan da ke faruwa suna nuni ne kawai da yanayin ɗan Adam.

Da yake ƙarin haske kan matsayar sa kan mulki, El-Rufai ya ce ba ya son siyasa, inda ya kwatanta wasu ‘yan siyasa da ‘yan wasan kwaikwayo.

“Haƙiƙa, ban san yadda zan yi riya ba. Wasunmu sun iya wasan kwaikwayo na Nollywood a harkokin mulki, inda wasunmu ba su iya ba,” inji shi.

A ɗaya ɓangaren kuma, tsohon gwamnan Jihar Kaduna ya ce, ba zai yi gudun hijira ba duk da raɗe-razin da ake yi na cewa ana shirin kama shi tare da azabtar da shi.

El-Rufai ya fazi haka ne a martanin da ya mayar a shafinsa na ɗ bayan wani mai amfani da shafin ya wallafa cewa ya samu bayanai masu ƙarfi da ke nuna ana shirin kama Ei-Rufai.

”Na daɗe ina jin waɗannan raɗe-raɗin kan kama ni da tsare ni da kuma azabtar da ni a wani ɗakin azabtarwa da ke ofisihin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro (wurin da ake zargin an azabtar ta Emefiele domin ya bar aiki a matsayin gwamnan CBN), tun watan Yulin 2024 lokacin da aka fara yaɗa rahoton majalisar dokokin jihar Kaduna” inji shi.

Ya kuma ce an aika irin waɗannan sakonnin barazanar ta hanyar abokai da ’yan uwanshi da dama saboda ana so ya yi ji tsoro ya yi gudun hijra da kanshi, sai da Ei-Rufai ya ce ”ba zan yi hakan ba”.

Ya ce, kafin ranar 20 ga watan Fabrairu zai dawo Nijeriya, ya kuma ce ya dakatar da karatun da yake yi da kuma shirin koyon wasu harsuna zai dawo gida Nijeriya, domin a cewarsa ba zai ci gaba da yin shiru ba.

Ei-Rufai ya kuma ce kamawa da tsarewa da kuma azabtar da abokan hamayya a siyasa ba sabon abu ba ne, ”ni kaina an kama ni kuma an kulle ne sau uku a baya saboda bayyana ra’ayi na kan gwamnatocin baya,” a cewarsa.