
Daga BELLO A. BABAJI
Dakarun sojoji sun yi nasarar kama wani soja mai suna Nathaniel Jeremiah, a Tasha Borno Express dake Maiduguri, bayan samun sa da wasu haramtattun alburusai.
Wata majiya ta sirri ta shaida wa Zagazola Makama cewa, sojan ya ɗauki hutu ne na ƙaramin lokaci da nufin zuwa Jihar Adamawa inda aka kama shi yayin da ya ke ƙoƙarin karɓar tikitin mota a tashar.
A lokacin da ake binciken sa, jami’an tsaro sun gano alburusan 7.62mm guda 89 a ƙunshe cikin jakarsa.
Daga nan sai aka gaggauta garzayawa da shi ofishin hukuma don gudanar da bincike akan sa.
An kuma miƙa alburusan ga hukumomin da suka dace don faɗaɗa bincike a kai.
