An kashe jami’an kwastom biyu an gudu da bindiga a Kebbi

Daga JAMIL GULMA a Kebbi

Waɗansu da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne sun kashe jami’an kwastom guda biyu kuma sun arce da bindiga qirar AK47 guda ɗaya a yayin da su ke sintiri a kan hanyar Ɗakingari zuwa Koko da misalin ƙarfe ɗaya da rabi na daren Alhamis ɗin da ta gabata.

Gwamnan jihar Kebbi Malam Nasiru Idris ya nuna rashin jin daɗinsa dangane da wannan ɗanyen aiki jim kaɗan bayan Sallar jana’izar su a harabar asibitin tunawa da Sir Yahaya da ke garin Birnin Kebbi a ranar Alhamis.

Malam Idris ya aike da saƙon ta’aziyya ga hukumar kwastom da kuma iyalan waɗanda suka rasu.

Ya sha alwashin haɗa hannu da duk jami’an tsaro da ke aiki a cikin jihar Kebbi don tabbatar da an samu tsaro da kuma zaman lafiya a jiha.

Jami’an kwastom da suka rasu sun haɗa da Abdullahi Mohammed, mataimaki na II da Sufeton kwastom A. K. Shehu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *