EFCC da CCB sun gayyaci Muhuyi Rimingado don amsa tambayoyi

Daga BASHIR ISAH

Hukumar yaƙi da rashawa EFCC da takwararta ta kyautata ɗa’ar ma’aikata, CCB, sun gayyaci Shugaban Hukumar Sauraren Ƙorafe-ƙirafe da Yaƙi da Rashawa na Jihar Kano (PCACC), Muhuyi Rimingado, don amsa tambayoyi kan batun kuɗaɗen hukumar.

A baya-bayan nan aka ji Rimingado na cewa yana gudanar da bincike kan faifan bidiyo da aka yaɗa mai alaƙa da tsohon Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje mai nasaba da cin hanci Dala.

Ganduje ya samu umarnin kariyar da ta hana hukumar yaƙi da rashawa ta bincike shi da iyalinsa da dukkan masu riƙe da muƙaman siyasa a ƙarƙashinsa.

Sai dai kuma a wani al’amari mai kama da martani ga Gandujen, hukumomin EFCC da CCB sun ƙaddamar da bincike kan Rimingado da ayyukansa a hukumar.

Cikin wasikarta mai ɗauke da kwanan wata 8 ga Agusta, EFCC ta ce: “Hukumar ta gayyato wani bincike da take buƙatar ƙarin haske daga ofishinka.

“Bisa wannan dalili ake buƙatar ka miƙa Daraktan Kuɗi don ba da bayani…..ya zuwa ranar 29 ga Agusta a Abuja…”

Cikakken bayani game da kuɗaɗen da Ofishin Akanta Janar ya sakar wa ofishin Rimingado na daga cikin batutuwan da EFCC ke neman bayani a kai da sauransu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *