Daga JAMIL GULMA a Kebbi
Rahotanni daga garin Kangiwa da ke jihar Kebbi sun bayyana cewa da sanyin safiyar Juma’ar nan an yi bata-kashi tsakanin sojojin Nijeriya da waɗansu ƴan bindiga da a ke sa ran mayaƙan lakurawa ne inda sojojin Nijeriya suka sami galaba kan su suka kashe da dama daga cikin lakurawan yayin da sauran suka gudu da raunuka.
Malam Yusuf wani mazauni garin na Kangiwa ya shaida wa waƙilin blueprint Manhaja da cewa kwanakin nan suna ganin mayaƙan suna shawagi a yankin ba dare ba rana a kan babura ɗauke da mutane biyu ko uku da su ke sa ran sun dawo yankin ne saboda matsin da su ke fuskanta daga Sojoji a yankin jihohin Katsina da Zamfara.
