Gidauniyar jinƙai ta Ɗahiru Mangal ta fara tantance masu lalurar gwaiwa a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a katsina

‎Gidauniyar jin ƙai ta Ɗahiru Bara’u Mangal Foundation ƙarƙashin jagorancin Alh. Ɗahiru Mangal ta fara gudanar da tantance masu lalurar gwaiwa da ƙaba a Katsina.
‎
Gidauniyar ta fara gudanar da tantance masu fama da wadannan lalura a babban asibitin Katsina (General Hospital).
‎
‎Da yake bayyana ma manema labarai yadda aikin ke gudana, ɗaya daga cikin ’yan kwamitin amintattu na gidauniyar Alhaji Hussaini Kabir, ya bayyana cewa” Wannan aiki ana gudanar da shi ne ƙarƙashin wannan gidauniya ta Mangal Foundation shekaru da dama kuma kyauta .
‎
‎Hussaini ya ƙara da cewa aikin yana kasancewa ne lokaci zuwa lokaci. “Kamar yadda kuke gani, ana tantance masu lalurar wanda bada jimawa ba za ayi masu aiki wasu kuma ana basu magani kyauta ƙarƙashin kulawa da ɗaukar nauyin Alh. Dahiru Mangal,”Inji Kabir.
‎
‎Sama da mutum 700 za su amfana da aiki a yayin da wasu cikin su zasu karɓi magani waɗanda lalurar ba tayi ƙarfi ba kyauta daga wannan gidauniya, Bayan wannan aiki kuma, gidauniyar na ɗaukar nauyin wasu aikace-aikace irin su aikin ido, fitsari da sauransu.
‎
‎Likitocin da ke gudanar da aikin sun bayyana cewa aikin yana tafiya yadda ya kamata, inda ake sa ran kammala shi cikin lokaci. Sun kuma yaba da yadda gidauniyar ta tanadi duk abubuwan da ake buƙata wajen aiwatar da aikin.
‎
‎Wasu daga cikin waɗanda suka amfana sun nuna jin daɗinsu ga Alh. Dahiru Bara’u Mangal, tare da yi masa addu’o’i na musamman bisa wannan gudummawa da ya yi musu.

By ukarofi