An kori ɗan Osama Bin Laden daga Faransa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Hukumomin ƙasar Faransa sun umarci Omar, wanda ɗan sanannen Shugaban ƴan ƙungiyar Al-Ƙa’ida, Osama Bin Laden ne da ya fice daga ƙasar.

Omar, mai shekaru 43, an buƙaci ya yi hakan ne ta kafar sada zumunta kamar yadda Ministan Harkokin Cikin gida na ƙasar, Bruno Retailleau ya bayyana.

An haifi Omar ne a ƙasar Saudiyya wanda ya kuma taɓa zama a Sudan da Afghanistan.

Sun kuma rabu da mahaifin nasa a lokacin da ya ke da shekara 19 a duniya inda daga bisani a shekarar 2016 ya koma yankin Normandy da ke Arewacin Faransa.

Saidai, Minista Retailleau ya ce, a shekarar 2023, Omar bin Laden ya wallafa waɗansu bayanai a shafukansa na kafafen sada zumunta da ke goyon bayan ta’addanci.

By Babaji