
Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Ƴan sanda a Katsina sun daƙile yunƙurin da ƴan bindiga suka yi na sace mutane a ƙananan hukumomin Faskari da Ɗan-Musa.
A Ɗan-Musa, ƴan bindigar sun tare mata su biyu a ƙauyen Matarau da ke kan hanyar Ƴan-Tumaki zuwa garin Ɗan-Musa, inda ƴan sandan suka kai wa matan ɗauki tare da yin ɗauki ba daɗi da ƴan bindigar har sai da suka samu nasarar ceto matan.
A Faskari kuwa ASP Sadiq Aliyu wanda shi ne Kakakin ƴan sandan jihar, ya ce ƴan bindigar sun tare hanyar ƙauyen Marabar Bangare da Unguwar Kafa a kusa da ƴan Kara wanda bayan samun rahoton ne sai ƴan sandan suka kai ɗauki .
Bayan ɗauki ba daɗi da yan bindigar ne ƴan sandan suka samu galaba akan su inda suka tsere ɗauke da mayan raunuka.
ASP Sadiq ya ƙara da cewa, yan sandan sun sami nasarar ceto matan su biyu tare da ƙananan yaransu.
Kwamishinan ƴan sandan jihar, Aliyu Abubakar Musa ya yaba da ƙwazo da nuna ƙwarewa da jami’ansu suka nuna wajen tunkarar ƴan bindigar tare da ceto mutanen.
Ya kuma jaddada ƙudirin rundunar ƴan sanda a jihar na kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
