A ranar Talata ne Gwamnan Jihar Zamfara Dauda Lawal ya yi alhinin mutuwar jami’an tsaron al’umma ( Community Protection Guards) da ‘yan bindiga su ka yi wa kwantan ɓauna a garin Tsafe kamar yadda mai magana da yawun gwamnan Sulaiman Bala Idris ya fitar.
Lamarin ya faru ne a wani shingen jami’an da ke wajen garin Tsafe, inda ƴan bindigan su ka yi ma jami’an kwantan ɓauna su ka kashe su. Gwamnan ya bayyana wannan a matsayin tsantsar rashin imani, ya kuma jaddada cewa jami’an tsaro na bincike domin kamo waɗanda su ka yi wannan ta’addanci.
Gwamnan ya yaba da irin ƙoƙarin da jami’an tsaron al’ummar ke bayarwa da kuma irin jajircewa da su ke domin ganin sun kawo tsaro a Jihar Zamfara.
Jami’an da wannan iftila’i ya abkawa su ne, Nasiru Aliyu, Jabiru Hassan, Abdullahi Dangunde, Bashar Bawa, Mu’azu Musa, Anas Dahiru, Anas Yakubu da Lawalli Yunusu.
Gwamnan ya miƙa ta’aziyar shi ga iyalan mamatan da kuma alƙawarin bada gudunmuwar da ya dace ga iyalansu.
