Cire tallafin hajji: kuɗin aikin hajji zai kai Naira miliyan 10

Spread the love

Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON) ta bayyana cewa gwamnatin tarayya ba za ta bayar da tallafin kuɗin aikin hajji ga maniyyata ba a shekarar 2025.

Kamar yadda Jaridar Manhaja ta rawaito cewa tallafin gwamnati yawanci yana zuwa ne ta hanyar rage farashin dala da ke bai wa maniyyata damar samun dala a farashi mai rahusa daga Babban Bankin Nijeriya (CBN).

Wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Fatima Sanda Usara, ta fitar ta ce a shekarar 2025, “Ba za a samar da wani farashi na musamman daga gwamnati don biyan kuɗin aikin hajji ga maniyyata ba, ko dai a ƙarƙashin gwamnatocin jihohi ko kamfanoni masu zaman kansu.”

Wannan yana nufin cewa idan Naira ta cigaba da kasancewa a farashin N1,650 kan kowacce dala, kowanne maniyyaci zai biya kusan Naira miliyan 10 don kuɗin aikin hajji, kasancewar maniyyata suna biyan akalla dala $6,000.

Duk da cewa NAHCON ba ta bayyana kuɗin aikin hajji na shekarar 2025 ba tukuna, Hukumomin aikin hajji na jihohi sun fara buƙatar maniyyatan da suka nufa aikin hajji su biya Naira miliyan 8.5 a matsayin ajiyar farko kafin a bayyana kuɗin aikin hajji.

By ukarofi