An kama mai unguwa da laifin ba ‘yan ta’adda bayanan sirri a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina.

‘Yan sanda a garin runka na ƙaramar hukumar Safana sun kama mutane biyu a cikin su har da mai unguwa da taimakawa ‘yan ta’adda da bayanan sirri.

Mai magana da yawun ‘yan sanda ASP Abubakar Sadiq Aliyu ya bayyana haka a lokacin da ya gabatar da masu laifin a gaban manema labarai.

Mai unguwar ƙauyen Runka Usman Adamu mai shekara 45 da haihuwa ya tabbatar da zargin da ake masa, ya bayyana wa BBC cewa abokin hirar sa Rabe ne ya gabatar dashi ga ɗaya daga cikin ɓarayin daji mai suna Umar.

Ya kuma tabbatar da bada bayanan sirri da shi ɗan bindigan da ya kai ga sace mutum biyu kuma a cewar sa, shima abokin sa Rabe yayi sanadiyar sace mutane biyu.

Sai dai mai unguwar yace har yanzu bai karɓi ko kobo daga hannun ‘yan bindigar ba bayan ya taimaka masu.

ASP Abubakar Sadiq yace ‘yan sanda za su cigaba da bincike da zarar sun gama za su gurfanar da su a kotu.

By ukarofi