Jami’ar koyon kiwon lafiya a Katsina za ta fara karatu kafin ƙarshen shekara

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Shugaban kwamitin TETFUND a majalisar dattijai sanata Muntari Ɗandutse ya sanar da cewa shirye shirye ya kammala na fara karantar wa a jami’ar koyon kiwon lafiya na garin Funtua a Jihar Katsina.

Ya ce ɗalibai 60 za su fara karatu a kowane tsangaya da hukumar kula da jami’o’i ta ƙasa ta amincewa.

Sanata Ɗandutse ya ce tuni gwamnatin Jihar Katsina ta amince da bawa jami’ar Naira biliyan biyu domin fara wasu aikace aikace na fara zangon karatu a jami’ar.

Sanatan ya yaba da irin kyakkyawar shugaban ci na Malam Dikko Raɗda akan ƙoƙarin da yake na inganta harkar ilimi a Jihar Katsina.

Sanata Ɗandutse wanda yake wakiltar mazaɓar shiyar Funtua ya yi kira ga al’ummar shiyar da mutanen jiha baki ɗaya da su bai wa gwamnatin Dikko Raɗda baya wajan ƙoƙarin da yake na bunƙasa jihar.

Ya kuma taɓo wasu nasarori da ya samu a tsawon zaman sa a majalisa da suka haɗa da samar wa matasa masu sana’ar POS da kuɗi dubu hamsin kowannen su don su fara harkan kasuwanci a ƙananan hukumomi 11 na shiyar Funtua.

Sauran sun haɗa da gina asibitoci da samar da motoci ga jami’an tsaro da kuma tallafawa da keke NAPEP da babura ga matasa domin su bunƙasa sana’arsu.

Yace ya gina ofishin yan sanda a ƙaramar hukumar Ƙanƙara da Malumfashi da kuma gina azuzzuwan karatu a ƙananan hukumomin Matazu da Faskari da Ɗanja da kuma cibiyar koyon sana’o’i a ƙaramar hukumar Musawa.

Sanatan wanda yana wannan bayani ga wasu al’ummomin sa a garin Funtua yayi alƙawarin kawo ababen more rayuwa da samar da aikin yi ga matasa a yankin sa.

By ukarofi