An kori ’yan sandan da suka harba harsashi a iska lokacin rakiyar Mawaƙi Rarara

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya ta kori wasu jami’ai uku da suke rakiya da gadin fitaccen mawaƙin Kano nan, Alhaji Dauda Kahutu Rarara, daga bakin aiki bisa samun su da laifin harbi ba bisa ƙa’ida ba, cin zarafin mutane, rashin ɗa’a, da almubazzaranci da harsashi.

A cewar jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, Muyiwa Adejobi, jami’an uku, Sufeta Dahiru Shuaibu, Sajan Abdullahi Badamasi, da Sajan Isah Danladi sub kasance tare da Rarara akan aikin rakiya.

“A yayin da suke gudanar da aikinsu a ranar Juma’a 7 ga Afrilu, 2023 a ƙauyen Kahutu da ke Jihar Katsina, jami’an sun yi ta harbin bindiga zuwa sama duk da dokar ’yan sanda na hana harbe-harbe a iska, wanda hakan ya sava wa tsarin aiki da kuma umarnin rundunar da abin ya shafa domin taron jama’a a wurin ya haɗa da mata da yara.

“Ayyukan ba kawai laifi ba ne da rashin ɗa’a amma kuma abin kunya ne ga rundunar da qasa baki ɗaya,” in ji Adejobi a wata sanarwa a ranar Alhamis.

Wani shaida na bidiyo ya yaɗu a shafukan sada zumunta kuma hukumomin ‘yan sanda sun gurfanar da mutanen uku a cikin tsari mai kyau da shari’a kuma an same su da laifin.