2023: Tinubu ya shiga jerin mutane 100 mafi tasiri a duniya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Zaɓaɓɓen Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu ya shiga cikin jerin mutane 100 da suka fi tasiri a mujallar Time Magazine ta 2023.

A duk shekara-shekara Mujallar Time na fitar da jerin mutane 100 mafi tasiri da suke bada gudunmuwa a duniya, ba tare da la’akari da sakamakon ayyukansu ba.

Jerin sunayen mutanen 2023 da mujallar ta fitar jiya Alhamis, sun kasu ne zuwa ɓangarori kamar haka: Jagorori, shugabanni, masu fasaha, masu ƙirƙire-ƙirƙire, da kuma ginshiƙai.

Tinubu, wanda ya lashe zaɓen Shugaban Ƙasa da aka gudanar a Nijeriya a ranar 25 ga watan Fabrairu, an saka shi ne tare da Shugaban Ƙasar Amurka, Joe Biden; Shugaban Brazil, Luiz Inácio Lula da Silva; Uwargidan Shugaban Ƙasar Ukraine, Olena Zelenska; a tsakanin sauran shugabannin duniya.

Rahoton ya bayyana Tinubu wanda za a ƙaddamar da shi a ranar 29 ga Mayu a matsayin “ɗan takarar da ya daɗe a cikin siyasa”.

Rahoton ya kuma ce da alama Tinubu yana sane da gadon da za a bar masa da suka haɗa da “rikitattun al’amura a cikin ƙasar da ta wargaje, da suka haɗa da cin hanci da rashawa, tada ƙayar baya da sunan addini da ƙabilanci; da ƙarancin kuɗi, man fetur, wutar lantarki da kuma taɓarɓarewar tattalin arziki”.