Batun inganta tsaro a mulkin Buhari

A lokacin da wa’adin mulkin Shugaba Muhammadu Buhari na biyu ke daf da ƙarewa, jama’a da dama ma cigaba da tafka muhawara akan batun tsaro a ƙasar cikin ’yan shekarun baya-bayan nan.

A hirar da ya yi a gidan talbijin ta Channels a ranar Litinin ɗin makon nan, Mai Magana da Yawun Shugaban Buhari, Femi Adesina ya ce, Muhammadu Buhari zai bar Nijeriya cikin aminci da gagarumin ci gaba a ɓangaren tsaro, idan an kwatanta da yadda ya same ta a farkon mulkinsa.

Kalaman Femi Adesinan dai sun jawo cece-kuce a tsakanin al’ummar ƙasar, ciki har da masana harkokin tsaro, inda ake ci gaba da tsokaci.

Wasu masana kamar Dakta Kabiru Adamu na da ra’ayin cewa Shugaba Buhari ya yi ƙoƙari a fannin tsaro, musamman ma ƙoƙarin ya nuna a wa’adin mulkinsa na biyu da ke daf da ƙarewa.

Mai sharhin kan harkokin tsaro a yankin Sahel ya ce, Buhari ya kuma yi ƙoƙari wajen taimaka wa hukumomin tsaron Nijeriya ta hanyar sayo sabbin kayan aikin sojoji da inganta horar da dakarun tsaro.

Ya ƙara da cewa, a ƙarƙashin gwamnatin Buhari, Nijeriya ta yi bitar yawancin dokokin da suka kafa hukumomin tsaronta, abin da aka ɗauki tsawon lokaci ba a yi ba, musamman dokar da ta kafa rundunar ’yan sandan ƙasar, wadda rabon da a yi mata bita tun zamanin mulkin mallaka.

A cewarsa, kafa hukumar taƙaita bazuwar makamai da bindigogi da Shugaba Buhari ya yi, shi ma muhimmin abu ne da ya taimaka matuka a ɓangaren tsaro.

Idan aka duba wani ɓangare, za a iya cewa tsaro ya inganta a ƙarƙashin mulkin Buhari. Amma idan aka duba qasar gabaɗaya, za a ga al’amura sun ƙara taɓarɓarewar a mulkin Buhari saboda yawan mutane da ake kashewa ya ƙaru, yawan ƙungiyoyi masu riƙe da makamai ya ƙaru, da kuma wuraren da ake kai wa hare-hare.

Idan aka ɗauki ɓangaren rikicin Boko Haram, za a ga cewa al’amura sun inganta a zamanin Muhammadu Buhari musamman Arewa maso Gabas.

Lokacin da Buhari ya zama shugaban qasa, bama-bamai na tashi a kusan ko ina a Nijeriya, inda ake samun hare-hare a Kano da Kaduna da Abuja da wurare daban-daban na arewacin Nijeriya.

Amma bayan hawansa, an yi nasarar daƙile rikicin Boko Haram bakiɗaya.

Duk da yake, barazanar ƙungiyar Boko Haram ta ragu, amma har yanzu suna kai hare-hare da kashe mutane a ƙauyuka.

Haka kuma ana iya cewa matsalar tsaron ta yaɗu daga Arewa maso Gabas, zuwa wasu wurare na Arewa ta Tsakiya da kuma Arewa maso Yamma waɗanda ba a samun haka kafin zuwan Buhari ba.

A lokacin mulkin Buhari ne matsalar ’yan bindiga ta ƙara ƙamari, duk da yake akwai su a baya, amma ba su da ƙarfin kai hari a kan makarantu da gidajen yari da kuma sansanonin jami’an tsaro.

A ƙarƙashin shugabancin Buhari ne aka sace dubban mutane duk shekara, sannan lokacinsa ne kuma ƙungiyar IPOB ta ɗauki makami da kuma kashe-kashen ’yan Arewa da ke yankin, da far wa ofisoshin INEC.

Game da kashe-kashen ‘yan Nijeriyan da ake ci gaba da samu, Dakta Kabiru Adamu, ya ce, a shekarar 2014-2015 lokacin da shugaba Buhari ya karɓi mulki, an samu kashe-kashe kusan 13,000.

Kuma a lokacin ne Boko Haram ta bayyana a matsayin ƙungiyar da ta fi aikata munanan kashe-kashe a duniya.

Amma ya ce, bayan zuwan Buhari, an samu raguwar kashe-kashen zuwa 6,000 ko 5,000 ko kuma 7,000.

Sai dai, ya ce ana cikin haka ne, sai aka samu canjin hare-haren ta’addancin da ake aikatawa, inda aka koma kai hare-hare zuwa Arewa maso tsakiyar Nijeriya da kuma Arewa maso yamma musamman jihohin Kaduna da Zamfara da Neja da Kogi har ma da Ondo da sauransu.

“Ayyukan ‘yan bindiga sun ƙaru a lokacin Buhari fiye da kafin hawansa kan karagar mulki, inda aka samu mace-mace 11,000 a 2022. Wannan ne ya sa akwai ayar tambaya a kan ikirarin da Femi Adesina ke yi,” in ji Dakta Kabiru Adamu.

Ya ce, bai dace Adesina ya yi irin wannan ikirari a wannan lokaci ba, ko da yake, in ji shi gwamnati ta yi huɓ asa, amma akwai kura-kurai da suka kamata a zauna a yi duba kansu da nufin kawo gyara.

Shi ma Barrister Bulama Bukarti, ya ce, alaaluma sun nuna cewa a shekara bakwai na mulkin Buhari, daga watan Maris ɗin 2015 zuwa Maris 2022, ƙungiyoyin ’yan ta’adda sun kashe ‘yan Nijeriya 55,430.

Ya ce, ko lokacin mulkin Goodluck Jonathan, ba a kashe ’yan Nijeriya masu yawa kamar a zamanin Buhari ba.

A cewarsa, bisa ƙididdiga aƙalla yanzu ana kashe mutum 7, 918 duk shekara a Nijeriya.

Femi Adesina dai a tattaunawarsa da Channels TV ya yi ikirarin cewa kafin zuwan gwamnatinsu, akwai shingayen bincike a yawancin sassan arewacin Nijeriya, lamarin da ya ce ko wannan ma wata manuniyar nasarar da aka samu ce.

Sai dai, Barista Audu Bulama Bukarti ya ce, abin da ya sa yanzu babu shingayen bincike shi ne saboda yaƙin da Nijeriya ke yi da ta’addanci ya sauya salo.

Ya ce, abin da ya sa ake da shingayen tsaro a hanyar Abuja zuwa Kano da hanyar zuwa Maiduguri da kuma Gashua, shi ne Boko Haram a lokacin ta matsa da kai hare-haren bam a cikin garuruwa.

“Yanzu kuma hare-haren sun fi karkata ne kan ƙauyuka musamman a jihohin Zamfara da Kebbi da Sakkwato da Kaduna da kuma a yankin Arewa maso Gabas,” in ji Bukarti.

“Ba wai babu barazanar tsaro ba ne a halin yanzu, amma salon faɗan ne ya canza.”

Batun taɓarɓarewar tsaro, ya haddasa wa Nijeriya gagarumar koma-baya ta fuskar tattalin arziki da ci gaban ƙasa.

Matsalar kuma ta haifar da ɗumbin matsaloli ga ‘yan ƙasar.

Dubban faruruwan ‘yan Nijeriya ne suka tsere daga gidajensu zuwa gudun hijira a jihohi kamar Borno da Yobe da Adamawa da Zamfara da Katsina da kuma Neja.

An rufe makarantu masu yawa bayan ’yan ta-da-ƙayar-baya da ‘yan fashin daji sun ƙaddamar da munanan hare-hare da sace ɗaruruwan ɗalibai don neman kuɗin fansa.

Ɓangaren tattalin arziki na daga cikin mafi shan wuya sanadin hare-haren ta’addanci.

Hukumomi sun riqa rufe kasuwanni saboda hare-haren da Boko Haram ta riqa kai wa a Arewa Maso Gabas.

A Arewa maso yamma kuwa, ayyukan ‘yan fashin daji sun jawo rufe kasuwanni don hana musayar kayan sata da sace kayan abinci da na masarufi da kuma ‘mai gabaɗaya’ mutanen gari.