A bar Abure a kan kujerarsa

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Duk mai bin kafafen labaru ko sha’awar halin da a ke ciki kan siyasar Nijeriya bayan babban zaɓe musamman na neman shugabancin Nijeriya da a ka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu zai iya cin karo da labarin damɓarwar shugabancin ɗaya daga jam’iyyun adawa wato jam’iyyar Leba. Wasu na son ture shugaban jam’iyyar Julious Abure daga karagarsa. Ita kan ta jam’iyyar ba sabuwa ba ce amma a gaskiya ta ɗauki hankali ne a matakin tarayya a takarar da Peter Obi ya yi na neman shugabanci inda ya zo na uku da ƙuri’u fiye da miliyan 6.

Matuƙar ba wani abu ne ya faru ya canja matsayin jam’iyyar ba to za ta cigaba da tasiri a labaru har zuwa zaɓen 2027 inda za a gane shin ta na cikin uku mafiya tasiri ko dai wani abu daban zai fito. Ko a yanzu za a dama da jam’iyyar a Majalisar Dattawa da wakilai kazalika ɗan takarar ta Otti ne ya lashe zaɓen gwamnanm jihar Abia.

Haƙiƙa har yanzu za a ce APC ke jan zaren ta ko ya tsinke ko an sake ƙulla shi tun bayan da ta ɗare madafun a zaven 2015 bayan mulkin PDP na tsawon shekaru 16. Tun ma ai daga nan ita ma PDP ta dawo ta biyu a matsayin mafi girman jam’iyyar adawa.

Ƙarfin jam’iyya kan iya jefa shugabannin ta a cikin riciki don hakan ya faru a PDP in an tuna yanda tsohon shugaba Jonathan ya jagoranci kwaɓe tsohon shugaban jam’iyyar Bamanga Tukur da hakan ya kawo tsohon shugaban jam’iyyar Ahmed Mu’azu da a ke yi wa taken mai sauya salon wasa “GAME CHANGER” amma in an tuna wasan ko gasar zaɓen ba ta tsallakar da PDP ba.

Hakanan APC ma da ta karɓa mun ga yanda tsohon shugaban jam’iyyar John Odiegie Oyegun ya nemi ƙarin shekara ɗaya bayan shugaba Buhari ya janye goyon baya ga shugabancin jam’iyyar amma hakan bai yiwu ba ƙarshe a ka kawo Adams Oshiomhole wanda ya so daɗewa kan karaga amma ina shi ma ya sa zargi cewa ya na taka dokokin jam’iyya da raina mutane ga zargin rub da ciki kan dukiyar jam’iyya.

Hakanan shugaba Buhari da kan sa ya sanar da sauke shi da hakan ya kawo riƙon ƙwarya na tsohon jagoran jam’iyyar gwamnan jihar Yobe mai ci Mai Mala Buni. Za mu tuna da yadda kwamitin Buni ya jagaoranci jam’iyyar har wasu su ka kauro jam’iyyar cancak ciki har da gwamnan jihar Zamfara mai barin gado Bello Matawallen Maradun.

A wani lokaci har gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello a ka yayata ya zama shugaban jam’iyyar amma daga bisani a ka samu sahihin bayani da ya kai ga gudanar da babban taron jam’iyyar inda ɗan takarar shugaba Buhari wato tsohon gwamnan Nasarawa Abdullahi Adamu ya zama shugaban jam’iyyar da zuwa wannan rubutu shi ke kan gado.

Shin zai ɗore kan mulki ko kuwa akasin hakan lokaci ne zai nuna. Kai ai tsarin siyasar Nijeriya kamar abun da ya faru ga wancan sai ya faru ga wannan. Tsarin da ya shafi PDP daga 1998 zuwa 2015 ya ke maimaita kan sa a jam’iyyar da ta karɓi ragama ko da ma za a ga da wani salon daban.

Shugabannin jam’iyyar adawa ta Leba na jihohi sun mara baya ga shugaban jam’iyyar Julious Abure da umurnin kotu ya dakatar.

Hakan ya jawo damɓarwa a tsakanin ɓangarorin biyu har sai da ƙungiyar ƙwadago ta fitar da matsaya.

Tun farko waɗanda su ka samu umurnnin kotu na dakatar da Abure sun yi dafifi a helkwatar jam’iyyar don hana Abure jagaoranci.

Shugabannin jihohin sun ce waɗanda su ke adawa da Abure na halin dakatarwa ne kafin su dau matakin don haka ba su da hurumin hakan.

A sanarwa daga shugaban ƙungiyar ƙwadago NLC Komred Joe Ajero da ke mallakar jam’iyyar ta Leba, ƙungiyar ta ce Abure ta sani a matsayin shugaba.

Jami’in ƙungiyar Komred Nasir Kabir ya yi ƙarin bayani, ya na mai cewa tuni ƙungiyar ta ɗau matakan shawo kan waɗanda ya ayyana da ’yan kutse.

Don haka shugabannin na jihohi sun zargi masu adawa da Abure da neman dakatar da yunƙurin Leba na ƙalubalantar sakamakon zaɓen 2023 ne.

A nan kakakin kamfen ɗin ɗan takarar shugaban ƙasa na Leba Peter Obi wato Yunusa Tanko ya ƙarfafa cewa an sa Abure a gaba ne don daqile ƙarar jam’iyyar a kotu, wato ma’ana barin Abure ya cigaba da jagoranci zai haddasa cikas ga masu son yin ƙafar angulu ga ƙarar da jam’iyyar ta shigar da ke neman a soke nasarar Bola Tinubu na APC a zaven 2023.

In an samu haka ma bai zama baƙon abu a siyasar Nijeriya ba don bayan zayven 2007 shugaba Buhari ya garzaya kotu don ƙalubalantar ayyana marigayi Umaru ’Yar’adua a matsayin wanda ya lashe zaɓe. A lokacin shugabannin jam’iyyarsa ta NNPP karkashin Chief Edwin Omo Ezeoke su ka janye goyon bayan su ga zuwa kotu su ka kuma haɗa kai ga jam’iyyar PDP inda har su ka amfana da wasu mukamai a gwamnatin da a ka zayyana da ta haɗin kansa da shugaba ’Yar’adua ya kafa.

A tsarin matuƙar masu adawa da Abure su ka yi nasara kuma su ka gwale Peter Obi da mara baya ga Tinubu, ba zai zama abun mamaki ba in an kafa gwamnati a ɗau wasun su a ba su mukamai. In haka ya faru ba sabon abu ba ne sam a tarihin zaɓe da gwamnatocin farar hula na Nijeriya.

Ai sauya sheƙa zuwa gwamnati da ke gado al’adar ’yan siyasa ne ko kuma ka ga mai matsayi irin na gwamna ya yi wuf ya fice daga jam’iyyar sa zuwa jam’iyya mai riƙe da madafun tarayya wai kar ya zama cikin mararsa rinjaye. Da rinjaye ko ba rinjaye matuƙar ɗan siyasar da ya samu wata kujera zai riƙe adalci da gaskiya to har kullum zai iya samun nasara.

Ita kuma nasarar nan ba wai lalle maƙalewa a kan mulki ba a’a zama mai mutunci a wajen jama’a ko masu zaɓe. Ina ribar mutum ya maqale kan mulki wataran kuma a samu tsautsayi ya bari jama’a na ƙin jinin sa ainun har ma ba sa son ganin sa ko jin maganarsa.

In dai da gaske dimokraɗiyya gwamnatin jama’a ce to ya na dsa kyau duk wanda ya samu ka sa a kan kujera ya dage ya yi abun da mutane su ke so ba wai abun da zuciyarsa da ta wasu muƙarrabai ta raya ma sa ko mu su ba.

Shugabannin na Leba na jihohi sun aara da cewa ya dace kowa ya jira sai an kammla babbar shari’a kafin kawo kowane ƙorafi. Ba a taɓa samun a kotun Nijeriya an soke zaɓen shugaban ƙasa a ka sake zaɓe ko naɗa wanda ya shigar da ƙara ba, amma aƙalla waɗanda su ke marawa wanda ya shigar da ƙara kan jajantawa junan su cewa sun yi iya ƙoƙarin su har kotun Allah ya isa don haka za su jira sai wata dama ta samu.

Zuwa kotu har ƙarshe da shugaba Buhari ya dinga yi har ranar da ya samu nasara na daga dalilan da magoya bayan sa su ka amince da cewa shi jajirtacce ne wajen karɓa mu su haƙƙinsu ko da ma daga baya ko yanzu da ya ke shirin barin karaga farin jininsa ya sauka ainun.

INEC da jam’iyyar APC sun nemi kotu ta yi watsi da ƙarar Leba:

Hukumar zaɓen Nijeriya, INEC da jam’iyyar APC mai mulki sun buƙaci kotun ƙarar zaɓen shugaban ƙasa ta yi watsi da ƙarar da jam’iyyar Leba ta Peter Obi ta shigar don ƙalubalantar sakamakon ayyana Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaɓe.

In za a tuna Leba da PDP sun tinkari kotun zaɓen wato kotun ɗaukaka ƙara ta tarayya a Abuja don neman ta soke sakamakon zaɓen shugaban Nijeriya na watan Febrairu.

A buƙatar su daban-daban, hukumar zaɓe da APC sun nuna tamkar Leba na neman vata wa kotu lokaci ne.

INEC ta cr ta bi dukkan dokokin zaɓe wajen gudanar da babban zaɓen don haka ba wata hujja a ƙarar ta Leba.

Jam’iyyar Leba ta zargi hukumar zaɓen da APC da murɗe alƙaluman zaɓe don samun ayyana Tinubu a matsayin wanda ya samu nasara. Leba ta ce hukumar ta INEC ta saɓa alƙawarin amfani da na’urar BVAS wajen tura sakamakon zaɓe. Hakanan Leba ta yi zargin aringizon ƙuri’a da ya ƙara wa APC damar zarcewa kan mulki.

Kammalawa;

Ko wanda a ka ayyana ya lashe zaɓe ko bai lashe ba, da zarar ya sha rantsuwa to zai fara cinye wa’adin mulkinsa ne. Daɗin dimokraɗiyya ta na da wa’adin shugabanci ba kamar sarautar gargajiya ba da in mai sarauta ya dace sai ranar da rai ya yi halin sa. Don haka kar mutane su riƙa zama cikin baƙin ciki ko nuna juna kiyayiya maimakon hamayya kan lamura na zave tun da abun da mai wucewa ne.

In mutum ya shuka alheri a shugabanci tarihi ya tuna alherin sa hakanan in ya shuka sharri. Duk wanda bai samu nasarar lashe zaɓe ba, to bayan zuwa kotu in akwai hujja, ya koma wajen talakawa ya yi ta yayata manufofin sa a hankali har ranar da kusan kowa zai ce sai wane.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *