Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano
An naɗa fitacciyyar Malamar Jami’ar FUE Kano (Federal Uniɓersity of Education) Dakta Ambasada Lami Abba Isma’il a matsayin Garkuwar Marayun ɗɗanruwatan Sarkin Hausawan Afirka.
Naɗin ya biyo bayan irin gudunmawa da tallafawa marayu da sauran al’umma da take yi a matsayinta na malamar Jami’a kuma mai rajin inganta rayuwar al’umma ta hanyar tallafawa al’umma a ƙungiyoyi daban-daban a matakin jihar Kano da ma ƙasa baki ɗaya.
Ita dai Dakta Ambasada Lami Abba Isma’il na cikin sahun gaba a ɗade-ɗaden ɗanruwatan Sarkin Hausawa ya yi a ranar Lahadi da ta gabata, wanda aka yi a Unguwar Tudun Wada a ƙaramar Hukumar Nassarawa jihar Kano.
A jawabinta, Ambasada Lami Isma’il bayan naɗin, ta yaba wa ɗanruwatan Sarkin Hausawan Afirka kan wannan karramawa da ya yi mata, inda ta ce wata dama ce ta ƙarfafa gwiwa na cewa abin da ake yi har jama’a suka gani suka yaba “to Ubangiji Allah ya karɓa kuma ya fi al’umma yaba wannan aikin alkairi wanda ya ƙaddara ya yadda ya hore kuma masu aikin alkairi su aika ta don haka abun farin ciki ne sosai.”
A ƙarshe ta ce a matsayinta na malamar makaranta kullum burinta ta ga yara matasa sun samu ilimi da tarbiyya ta hanyar girmama na gaba da sanin ya kamata.
“Kuma ba shakka yadda muke koyar da ‘ya’yan al’umma haka muke koyar da namu domin an ce yi wa wani yi wa kai, domin kullum abin da yake faranta min rai a rayuwa in ga na farantawa marayun da sauran al’umma rai wannan abu yana faranta min rai.”
Ta kuma yaba wa ɗaukacin zuri’ar ta da iyalai da sauran abokan aiki na Jami’ar FUE tun daga kan shugaba da sauran abokan aiki manyansu da ƙananansu kan addu’a da nuna farin ciki da gudunmawa da su ka bayar na yin wannan naɗi cikin nasara da kwanciyar hankali a Kano.
