Daga MUKHTAR YAKUBU
Likkafar Mawaƙi Aminu Ladan Abubakar Ala ta ƙara ɗagawa zuwa mataki na gaba inda ya samu jakadancin Jami’ar Arewa maso gabas wato ‘North-Eastern University’ . Kamar yadda ya tabbatar a saƙon sa na ranar Juma’ar da ta gabata.
Aminu Ladan Abubakar Ala mai riƙe da sarautar Sarkin ɗiyan Gobir daga Masarautar Gobir Tsibirin Sarkin waƙar Masarautar Dutse kuma Dan Amanar Gidan Dabo
Ya wallafa cewar ” Saƙon Barka da Juma’a na wannan sati ya zo da busharar shaidar Jakadancin ‘Noth-Eastern University Gombe,” tare da hoton sa tare da Sarkin Gombe Alhaji Abubakar Shehu Abubakar tare da mataimakin Shugaban Jami’ar Danlawan na Gombe, suna ba shi takardar shaidar jakadancin wannan ƙasaitacciyar makaranta da ke shirin wakiltar Africa bakiɗaya ta fuskar ilimi.
Aminu Ladan Abubakar Ala ya ce,” Muna jaddada godiya musamman ga wannan ƙasaitaccen Sarki Mai ikon ƙasar Gombe gabaɗaya, tare da Hakiminsa ɗallawan Gombe, wanda shi ne ‘Pro Chancellor’ na wannan makaranta ta ‘North-Eastern University’ Gombe. Da addu’ar Allah ya fisshe mu kunyar juna, a bisa wannan nauyi da amana da aka damƙa mana. Daga nan na ke yi wa masoyana busharar aikin nan tare za mu yi shi har a kai ga nassara. Hasali ma saboda irin gogoriyo na ƙaunar da kuke nuna mini da shauƙin soyayyarku a kan ayyukan adabi shi ya sa aka bani wannan aiki mu fara shi tare. Na kuma san ba za a bani kunya ba, musamman masoyan nan nawa da ba dare ba rana ana tare cikin mu’amalantar juna, ba tare da jin ƙyashi ba.”
Jama’a da dama dai sun taya Mawaƙi Aminu Ladan Abubakar Ala murna tare da fatan alheri dangane da samun wannan matsayin jakadancin da ya yi.
