Hukumar tantance fina-finai ta mallaki hedikwata a Abuja bayan shekaru 30

Spread the love

Hukumar Tantance Fina-Finai da Bidiyo ta Kasa (NFVCB) ta samu hedikwatarta ta dindindin a Abuja bayan kusan shekaru 30 tana gudanar da aiki ba tare da na dindindin ba. Wannan ci gaban ya zama babban tarihi ga hukumar.

Wannan lamari ya tabbata ne a ranar Talata, lokacin da shugaban hukumar, Dakta Shuaibu Husseini, ya jagoranci tawagarsa wajen kai ziyarar ban girma ga Ministar Al’adu, Yawon Buɗe Ido, da Tattalin Arzikin Kirkire-Kirkire, Hajiya Hannatu Musa Musawa, domin nuna godiya bisa rawar da ta taka wajen tabbatar da mallakar wurin.

Dakta Husseini ya bayyana cewa, sabon ginin, wanda Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta kwace tun daga shekarar 2017, shi ne aka miƙa wa NFVCB sakamakon shawarwari da tallafin da ministar ta bayar.

“Mun gode miki, Mai Girma Minista, bisa taimako da shawarwarinki. EFCC ta ba mu wannan wurin zama wanda aka kwace tun 2017. Za mu yi wasu gyare-gyare, amma muna farin ciki domin bayan shekaru 28, a ƙarƙashin kulawarki muka samu mu mallaki na mu. Wannan tarihi ne ga hukumar,” inji shi.

Ya ce, ginin yana da isasshen sarari da za a kafa gidan tarihin NFVCB da aka daɗe ana fatan ganin kafa shi, wanda zai zama matattarar nuna al’adun Najeriya.

Husseini ya kuma sha alwashin cewa hukumar za ta ci gaba da mara wa minista baya tare da daidaita ayyukanta da manufofin ‘Renewed Hope Agenda’ na Shugaba Bola Tinubu.

A nata jawabin, Ministar Hannatu Musa Musawa ta yaba da jajircewa da kishin ƙasa da Dakta Husseini ya nuna tun bayan naɗa shi shugaba.

“Ina farin ciki da yadda kake da jajircewa da nasarar da kake samu wajen tafiyar da hukumar NFVCB. Tun daga lokacin da Shugaban Kasa ya naɗa ka, na tabbatar kai mutum ne na musamman, wanda ya dace a kira da ‘Ni ɗan Najeriya ne.’ Wannan sabon hedikwata na nuna bambanci mai girma a aikinmu. Ina alfahari da kai, kuma farin cikina ne kasancewa a wannan tafiya tare da kai domin za ka taimaka min wajen gudanar da aikina, mu kuma gaba ɗaya mu taimaka wa Shugaban Kasa ya cimma nasara,” inji ta.

A cewar NFVCB, nan gaba kaɗan za ta ƙaddamar da gidan tarihin nata a sabon hedikwatar tare da shirin gudanar da taron Digital Conference a watan Nuwamba. Dakta Husseini ya kuma gayyaci ministar da ta halarci taron domin ƙarfafa haɗin kai tsakanin hukumar da ma’aikatar.

Masu lura da masana’antar shirya fina-finai sun bayyana wannan mallakar hedikwata a matsayin gagarumin ci gaba ga sashen fina-finai da ƙirƙire-ƙirƙiren Najeriya, wanda ke ƙara samun karɓuwa a fagen duniya.

By ukarofi