An rantsar da Dauda Lawal a matsayin Gwamnan Zamfara

An rantsar da Dauda Lawal Dare a matsayin sabon gwamnan Jihar Zamfara a hukumance.

Bikin rantsarwar ya gudana ne a ranar Litinin a filin kasuwar baje koli da ke Gusau, babban birnin jihar.

Dauda ya zama sabon gwamnan jihar ne bayan da ya lashe zaɓen gwamnan jihar ƙarƙashin Jam’iyyar PDP inda ya samu ƙuri’u 377,726.

Dauda ya doke babban abokin hamayyarsa Jam’iyyar APC kuma gwamnan jihar a wancan lokaci, Bello Matawalle, wanda ya tsira da ƙuri’u 311,976.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *