Shugabancin Kano: Zan binciki bashin N241bn, cewar Abba Kabir ga Ganduje

Sabon Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sha alwashin gudanar da bincike kan bashin da gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta ciyo na Naira biliyan 241.

Gwamna Yusuf ya ce takardun bayanan gwamnati da Ganduje ya miƙa ta hannun Sakataren Gwamnatin Jihar mai barin gado, ba su wadatar ba.

Ya caccaki Ganduje kan rashin tasayawa ya miƙa ragamar mulki da kansa, amma ya wakilta wani maimakon haka.

A cewar Yusuf: “Takardun bayanan gwamnatin sun yi mana kaɗan. Haka ma bayanan kwamitin miƙa mulki ba su da yawa.

“Babu abin da za mu iya yi a matsayinmu na wakilan jama’a, ba za mu ƙi karɓar abin da aka miƙa mana ba, za mu duba lamarin.

“Za mu ɗauki mataki a inda muka gamsu, haka ma za mu ɗauki matakin da ya dace a inda ba mu gamsu ba,” in ji shi.

Yusuf ya yi wa Gandujen addu’ar Allah Ya saka masa da alheri bisa gwargwadon hidimar da ya yi wa jihar.

Tare da cewa, sun zo ne ba don su yi sata ko ƙwace filayen jama’a ba, “Mun zo ne don yin aiki, kuma da yardar Allah za mu cimma manufofin da muka tsara a cikin shekara huɗu.”