An rantsar da sabbin jagororin IMAN reshen asibitin Aminu Kano 

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano 

Bayan kammala wa’adin shugabancin ƙungiyar Likitoci Musulmi da Dakta Sule Abdullahi Gaya da mataimakansa, guda daga cikin jerin shugabanni da ƙungiyar ta yi tun kafuwarta a shekarar 1999, yanzu haka an ranstar da Dakta Abdulgaffar a matsayin sabon shugaban IMAN da mataimakansa, kamar dai yadda shugaban kwamitin amintattun ƙungiyar, Farfesa Musa Burodo wanda ya samu wakilcin Pharmcy Musa Abdullah, sakataren kuɗi na kwamitin amintattun IMAN wanda ya jagoranci rantsar da sabon shugabannin da aka yi a harabar AKTH Kano.

An dai kafa ƙungiyar likitocin Musulmi ne domin haɗa kan mambobinta don inganta ƙwarewarsu da kuma wayar da kan Musulmi da yaɗa bikin a tsakaninsu da bunƙasa ilimin kiwon lafiya da kuma bincike da wallafa shi domin amfani na wannan fagen na lafiya dai dai makamatansu.

Toron gabatar da rantsar da sabon shugabannin IMAN ya samu halatar babban jami’n kuɗi da mulki na IMAN wanda ya wakilci CMD Farfesa Sheshe da sauran manyan jami’an asibitin da ɗaukacin masu ruwa da tsaki na ƙungiyar na IMAN.

By ukarofi