Daga IBRAHIM MUHAMMAD
An rantsar da sabon Kwamitin riƙo na shugabancin yan kasuwar Kantin Kwari ƙarƙashin Alhaji Abdullahi Shariff Namalam da zai jagoranci ƙungiyar har zuwa lokacin da za a gudanar da zaɓe.
Taron rantsuwar an gudanar da shi ne a ma’aikatar Kasuwanci na jihar kano ranar talata ƙarƙashin jagorancin kwamishinan ma’aikatar Alhaji Shehu Wada Sagagi ya sami halartar ɗimbin yan kasuwar.
Sagagi ya nemi yan kasuwar su haɗa kai da kamfanonin ƙasashen duniya da suke mu’amala da su don jawo hankulansu wajen samar da wasu abubuwa da za su tallafawa cigaban kasuwanci da horar da matasa akan yanda za su amfani ci gaban kasuwanci a jihar Kano.
A jawabinsa manajan Darakta na hukumar kasuwar Kantin kwari.Hon.Hamisu Sa’ad Dogon Nama ya ce suna da kyakkyawan dangataka da yan kasuwar kuma suma ’yan kasuwa ne, ba baƙi ba, illa dai kawai shi yana wakiltar Gwamnati a kasuwar ne.
Ya ƙara da cewa, su kuma ƙungiyar yan kasuwa na wakiltar ’yan kasuwa ne don haka dukkansu abokan mu’amalar juna ne wajen gudanar da al’amuransu. Ita kasuwa tana ɗauke da al’umma ne kuma doka ta yarda su yi ƙungiya don kare muradunsu a matsayinsu na yankasuwa.
Manajan daraktan na hukumar gudanarwar kasuwar Kantin Kwari.Hon.Hamisu Sa’ad Dogon Nama ya ce ƙungiya tanada muhimmanci ita take wakiltar yan kasuwa domin a Kantin Kwari akwai yan kasuwa samada miliyan idan Gwamnati tana da wani abu, ba sai ta tara su ba, ta ƙungiya za ta yi magana da su, suma idan suna da buƙata daga gwamnati ta ƙungiya zasu isar, ita za ta zama a tsakiya ne tsakanin yan kasuwa da Gwamnati.
Shima a nasa jawabin sabon Shugaban kwamitin riƙo na shugabancin ƙungiyar kasuwar Kantin kwari Alhaji Abdullahi Sharif Namalam yace samar da wannan kwamiti wani abin tarihi ne ga kasuwar suna kyautata zaton in Allah ya yarda wannan tsarin da aka zo da shi Allah zai fitar da su kunya.
Ya kuma yaba da irin albishir da kwamishinan kasuwanci ya yi musu na cewa Gwamnatin jihar kano za ta kawo tsare tsare na bunƙasa cigaban kasuwar, za su mara mata baya domin tabbatarda nasara da yardar Allah.
Alhaji Abdullahi Sharif Namalam yace burinsu a ƙarƙashin kwamitin su sami haɗin kai daga hukumar kasuwar da ƙananan ’yan kasuwa da manya a kasuwar Kantin Kwari domin cigaban kasuwar.
