An rantsar da shugaban ƙungiyar GDF

Daga MUHAMMAD MUJITABA

A cikin makon nan ne aka rantsar da shugabanin haɗaɗiyar ƙungiyar cigaban unguwar gwammaja da ke Dala ta Jihar Kano watou ‘Gwammaja Development Forum’ ƙarƙashi shugabancin Abdulshakur Tahir, a matsayin babban shugaban GDF na farko.

Shugabanin da aka zaɓa kuma aka rantsar da su ne Sani Usman, mataimakin shugaba, Fatihu Sani Imam Sakatare, Baffa Ismail, mataimakin sakatare, Abba Rabiu Ali, Sakataren kuɗi, Mujittafa Ismail, ma’ajin kuɗi, sauran dai su ne akwai Mustapha Abdullahi a matsayin jami’in hulɗa da jama’a, Fatihu Ashiru Lawan, Jamil hulɗa da jama’a na biyu, jami’in kula da jin daɗi  ’yan qungiyar GDF shi ne Abubakar Tahir Musa, mai binciken kuɗi, Abubakar Haladu, akwai mai tsawatarwa na GDF Khamis Abubakar , sai Sadeek Bala Usman a matsayin ’yan majalisar Dattawa na ɗaya a ƙungiyar su ne sai na biyu Shamsu Suleiman Ya’u na biyu Usaini Sani Adamu sai kuma yan majalisar Dattawa a qarshe GDF Bello Abubakar Muhammad. Waɗanan su ne shugabanin GDF 15 Da aka zaɓa kuma aka rantsar da su.

A jawabin sa bayan rantsuwar Abubakar Tahir ya ce, wannan ƙungiyar rukunin ƙungiyoyi ne na unguwanin ƙaramar hukumar dala masu yawa aka kirawusu da samar da wannan inuwa ta su kuma kowa ce ta na nan a matsayin ta na ƙungiyar wannan dai don ƙarfafa gwiwoyi da neman cigaba a koda yaushe don ciyar su  gaba a matsayin taimako ga al’umma da kuma ita kanta ƙaramar hukumar Dala bisa haɗin kai yan ƙungiya iyayan GDF na Dala waɗanda suka haɗa da shugabanin malamai masana da dai sauran masu kishin jama’a wanda kuma shugaban GDF ya yi alwashin aiki tukoro a matsayinsa na shugaban ƙungiya kamar yadda aka tsara.

An dai gayyato manya baƙi a wannan rantsuwa don sanya albarka da gabata da jawabai kaɗan daga ciki akwai Dakta Sidi Ahmad Dukawa.

Sauran sun haɗa da A.A. Ayagi, Farfesa Aliyu Suleiman, Dakta Balkisu Dahiru, Alhaji Bashir Ibrahim Gwamaja Alhaji Aminu Muktar da kuma Alhaji Uba Leda.