Shugaban ƙungiyar Fitiyanul Islam ya yaba da maulidin Ma’ahad Wailari

Daga MUHAMMAD MUJITABA

Sheikh Malam Tujjani Mai Salati Indabawa na daga cikin manya baƙi da suka halarci gagarimin taron Maulidi na makarantar Islamiyya mai suna Ma’ahad Sayyidina Usman Litahafizul Ƙur’an a karo na shida da ke unguwar wailari cikin ƙaramar hukumar Kumbotso Jihar Kano, wanda ya gabata a ranar Lahadi ta gabata a harabar makarantar.

Haka kuma ya nuna farin ciki da wannan maulidi wanda ya nuna da cewa abu ne mai falala a duniyarmu da lahirarmu. Kamar dai yadda malam Tujjani Mai Salati Shugaban Fitiyanu Islam ya nuna haka.

Shi ma a jawabin sa shugaban makarantar a Ma’ahad, Malam Abubakar Muhammad Darma ya ce, suna shirya wannan maulidi don cusa ɗalibai yara da manya ƙaunar Annabin Allah don haka ne su ke karanta tarihin ma’aikin Allah don a samu ilimi kyawawa ɗabi’u na gari kamar haƙuri, kyauta, zumunci, kunya, sanin  ya kamata irin na Manzon Allah (S.A.W), hakan zai sa yara da manyan zai sa ayi ko yi da shugaban halitta kuma shi ne burin mu na yin maulidi duk shekara kuma ba shakka wannan makaranta da wannan unguwata wailari kwaliya na biyan kuɗin sabolo a wannan aiki na mu.

Haka kuma ya yaba jama’ar unguwar da kuma mahalata wannan maulidi manya baƙi da sauran al’umma musamman irin su shugaban hukumar shari’a Khalifa Bashir Sheikh Tijjani Usman da Alhaji Muhammada Maigidan Nufawa, Shugaban Rabiɗatul Ittihad da kuma khadimul Nabiyu Alhaji Sani Kabiru Yakasai wanda aka fi sani da SKY da dai sauran manyan baqi da sauran al’umma.