An rufe Jami’ar FUDMA bayan kashe wani ɗalibi

Spread the love

Daga UMAR GARBA a Katsina

Hukumomi a Jami’ar gwamnatin tarayya ta Dutsinma (FUDMA) da ke Jihar Katsina, sun rufe makarantar, sakamakon zanga-zangar da ta ɓarke a jami’ar bayan da jami’an tsaron haɗin-gwiwa na Civilian Task Force suka harbe wani ɗalibi da ke ajin ƙarshe ( Level 400) a jami’ar.

Rahotanni sun bayyana cewa jami’an Civilian Task Force sun harbi wasu ɗalibai biyu bisa tunanin ‘yan bindiga ne, lamarin da ya yi sanadin mutuwar xaya daga cikinsu.

An harbe Sai’d Abdulkadir, ɗalibi da ke karatun digiri a fannin aikin noma, bayan da abokinsa ɗalibi ya goya shi akan babur.

Majiyar Blueprint Manhaja, ta bayyana cewa jami’an tsaron sun tsayar da ɗaliban a wani shingen bincike da suka kafa sai dai ɗaliban ba su tsaya ba lamarin da yasa jami’an tsaron CTF suka buɗe masu wuta.

Lamarin ya fusata sauran ɗaliban jami’ar inda suka yi gangami da yawa tare da tare babbar hanyar Dutsinma zuwa Katsina suna rera wakar neman a yi wa abokin karatunsu da aka kashe adalci.

Majalisar zartaswar jami’ar ta FUDMA, a cikin wata sanarwa data fitar ranar Litinin, ta sanar da rufe makarantar nan take tare da umurtar dalibai da su gagagauta barin harabar jami’ar kafin ƙarfe 6: 00 na yammacin ranar Litinin.

Jami’ar ta kuma buƙaci ɗaliban da su fara hutun tsakiyar zangon karatu ( Mid Semester Break) na mako guda daga ranar Litinin 24 ga watan Fabarairu.

Shugaban jami’ar Farfesa Armaya’u Hamisu Bichi ne, ya sanar da wannan mataki da majalisar zartaswar jami’ar ta ɗauka.

By Babaji