Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
A hirar da Kwamishinan Ƙidayar Jama’a da Gidaje na Tarayya da ke Jihar Katsina, Injiniya Bala Almu Banye, ya tabbatar da cewa za a gudanar da ƙidayar jama’a a cikin watan Afrilu na shekarar 2023.
Injiniya Bala Almu, wanda shi ne Zarman Katsina, ya yaba da yadda hukumar ta samu nasarar shirin na gwajin ƙidayar mutane da gidaje a shiyyar Daura.
Zarman na Katsina ya kuma ce za a gudanar da shirin ƙidayar jama’a da gidaje a ko’ina a cikin Nijeriya a watan Afrilu na shekarar 2023.
Ya kuma gode wa Shugaban Nijeriya, Muhammadu Buhari, kan irin tallafin da yake ba hukumar domin ganin ta cimma nasarar shirin na ƙidayar jama’a da gidaje da ke tafe a 2023.
Alhaji Bala Almu Banye ya ma ce tilas sai shirin ya sami cikakken goyon baya za a cimma nasarar da ake buƙata.
Kuma yana farin cikin sanar da mutanen Nijeriya cewa hukumar ta hanyar zamani kai tsaye za a ɗauki ma’aikatan da za su gudanar da shirin ƙidayar jama’a da gidaje mai zuwa.
Ya ma ce tilas za a ɗauki masu kula da shirin ƙidayar jama’a da gidaje wanda kowace jiha a ƙasar nan za ta rubuta buƙatar ta ga abin da take buƙata.
Alhaji Bala Almu Banye ya shaida wa manema labarai cewa, haƙƙin hukumar ne ta tura waɗanda za su koyar da yadda za a gudanar da shirin a yankunan karkara.
Ya kuma taɓo batun su kansu ma’aikatan da hukumar za ta tura domin ba da horo ga sababbin ɗauka, wanda abu ne mai matuƙar muhimmanci a gare su.
Shugaban Hukumar, Alhaji Bala Almu Banye, ya kuma yi wa ‘yan Nijeriya alƙawarin cewa matuƙar suka ba shirin ƙidayar jama’a da gidaje cikakke goyon baya.
Ya ce hukumar ba za ta yi wata-wata ba wajen ganin an ƙidaya kowa da kowa a shirin da ke tafe a watan Afrilu, 2023, musamnan ta hanyar zamani.
Daga baya kuma wasu daga cikin manema labarun sun yi wa Shugaban Hukumar tambayoyin da suka shafi aikin gudanar da shirin ƙidayar jama’a da gidaje a Jihar Katsina da ma ƙasa baki ɗaya.
