Gwamnati ta shigar da sabuwar ƙara a kotu kan Jagoran IPOB, Nnamdi Kanu

Daga WAKILINMU

Gwamnatin Tarayya ƙarkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari ta sake shigar da ƙarar jagoran masu fafutukar ƙasar Biyafara (IPOB) Nnamdi Kanu, kan wasu tuhume-tuhume guda bakwai da ta yi wa gyaran fuska.

Rahotanni sun nuna cewa ƙarar mai lamba: FHC/ABJ/CR/383/2015 da aka shigar a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, na ƙunshe da dukkan tuhume-tuhumen da aka yi wa Kanu a baya wanda kotu ta riga ta wanke shi a kansu.

Gwamnati ta sake maka Kanu a kotun ne kimanin wata ɗaya bayan da Kotun Ɗaukaka Ƙara ta wanke shi daga zarge-zargen da gwamnati ta yi masa a baya.

Gwamnati ta yi zargin Kanu wanda a halin yanzu yake tsare a hannun Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS), a matsayinsa na mai jagorantar haramtacciyar ƙungiya, an jiyo muryarsa a wani shirin da aka yi da shi a rediyo ya yi barazanar zai gama da duk wanda ya ƙi bin umarninsa na kowa ya zauna a gida a yankin Kudu maso Gabas.

Gwamnati ta shaida wa kotun sakamakon barazanar da Kanu ya yi, hakan ya tilasta wa makarantu da kasuwanni da bankuna da gidajen mai da sauransu rufe harkokinsu a wasu jihohi da ke Kudancin Najeriya, tare da jefa jama’a cikin mawuyacin hali.

Haka nan, Gwamnati ta yi zargin wani lokaci tsakanin 2018 da 2021, an ji jagoran na IPOB cikin wani shirin rediyo yana ingiza al’umma a kan su yi farautar jami’an tsaron Najeriya da iyalansu su kashe.

Wannan laifin dai gwamnatin ta ce hukuncinsa na ƙarƙashin Sashe na 1 (2) (h) na Dokokin Hana Ta’addanci wanda aka yi wa gyara na 2013.

Kazalika, gwamnatin na zargin Kanu da bai wa mambobin IPOB umarnin su haɗa bama-bamai, da sauransu.

A baya, Kanu ya musanta tuhume-tuhumen da gwamnati ta yi masa.

Alƙalin kotun, Mai Shari’a Binta Nyako, ta tsayar da ranar Litinin mai zuwa don lauyoyin ɓangarorin biyu su haɗu su yi wa kotun bayanin yadda za a samu mafita kan batun.