Atiku Abubakar ya ba da tallafin miliyan N50 ga waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa a Hadejia

Daga ABUBAKAR M. TAHEER

Ɗan takarar Shugaban Ƙasa na Jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar GCON, ya bada tallafin Naira miliyan 50 ga waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa a fadar Mai Martaba Sarkin Hadejia.

Cikin jawabinsa Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa sun zo jajantawa masarautar Hadeja ne ganin irin asarar dukiyoyi da rayuka da aka samu sanadiyar ambaliya.

Atiku ya ƙara da cewa, ya bada tallafin Naira miliyan 50 domin a raba wa waɗanda iftila’in ya shafa.

Da yake jawabi, Sarkin Hadejia, Alhaji Adamu Abubakar Maje CON, ya bayyana farin cikinsa da wannan ziyara ta Atiku, kana ya yi kira ga sauran ‘yan siyasa da su yi koyi da haka.

Cikin waɗanda suka yi wa Abubakar rakiya akwai Daraktan Yaƙin neman zaɓen Jihar Sokoto, Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal, Sule Lamido CON, Ambasa Iliyas Damagun, Alhaji Adamu Maina Waziri, Sanata Deno Malaye da dai sauransu.

Yayin ziyarar, ɗan takarar ya sami tarba mai armashi daga ɗimbin magoya bayansa daga cikin da wajen Jihar Jigawa.