Kotun Ɗaukaka Ƙara ta jinkirta hukunci kan dambarwar Machina da Lawan

Daga SANI AHMAD GIWA

Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke zamanta a Abuja a ranar Juma’a ta jinkirta yin hukunci kan ƙarar da Jam’iyyar APC ta shigar kan ɗan takarar Sanatan Yobe ta Arewa, Bashir Sheriff Machina.

APC ta kai ƙarar ne Kotun Ɗaukaka Ƙara inda ta buƙaci kotun ta yi watsi da hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ke Damaturu wadda Mai Shari’a Fadimatu Aminu ta bayyana Machina a matsayin ɗan takarar Sanata na Jam’iyyar APC a Yobe ta Arewa ranar 28 ga Satumba, 2022.

Shar’iar wadda Mai Shari’a a Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Abuja, Justice Monica Dongban-Mensen ta jagoranta, ta ce za ta yi duba a kan hukuncin da Babbar Kotun Tarayya da ke Damaturu ta yanke, wadda ta ayyana Machina a matsayin halastaccen ɗan takarar kujerar Sanatan Yobe ta Tsakiya.

Lauyan Machina, Ibrahim K. Bawa (SAN) a muhawarar sa, ya buƙaci Kotun Ɗaukaka Ƙara da ta yi watsi da ƙarar da aka shigar kan rashin cancanta, sannan ta tabbatar da hukuncin da Babbar Kotun Tarayya wanda ya ce ya yi daidai.

Bayan sauraron muhawarar lauyoyi, kotu ta ce za ta sanar da ranar yanke hukuncin ga dukkan ɓangarorin da abin ya shafa.

Machina dai ya lashe zaɓen fidda gwani da Jam’iyyar APC ta shirya a watan Mayu, 2022, a yayin da Sanata Lawan aka kara da shi a zaven fidda gwani na takarar kujerar Shugaban Ƙasa wanda jam’iyyar ta shirya a watan Yuni, 2022.

Sanata Ahmad Lawan ya sha ƙasa a hannun tsohon gwamnan Legas, Bola Ahmed Tinubu.

Kodayake, an ta ce wa Machina ya ajiye takarar sa ya bar wa Lawan, amma ya murje idanuwansa ya ce sam ba zai bar wa wani takararsa ba yana ji yana gani.

Duk da dambarwar da ake ta yi a lokacin, haka Jam’iyyar APC ta aike wa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC da sunan Sanata Lawan a matsayin ɗan takararta na Sanata mai wakiltar Yobe ta Arewa.

Kwanakin baya dai an jiyo Sanata Lawan ya furta cewa ya rungumi ƙaddara, ya bar wa Machina, inda kuma ya ce ba zai ɗaukaka ƙara ba.