An sace mutane 30 yayin da biyu suka rasu a harin ‘yan bindiga a ƙauyen Jihar Kogi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

‘Yan bindiga sun kai hari a ƙauyen Ayegunle-Igun da ke ƙaramar hukumar Kabba-Bunu a Jihar Kogi, inda suka halaka mutum guda tare da yin garkuwa da fiye da mutum 25 a wani hari da suka kai da tsakar dare.

Rahotanni sun ce maharan sun shiga ƙauyen ne tsakanin ƙarfe 2:30 zuwa 3:00 na dare, inda suka rika harbe-harbe tare da kutsawa gidajen jama’a.

Wani mazaunin yankin ya bayyana cewa maharan sun sace ‘yan uwansa biyu, yayin da wasu daga cikin mutanen da aka kama suka samu damar tserewa.

An kuma ruwaito cewa wani mazaunin ƙauyen ya rasa ransa yayin da yake ƙoƙarin tserewa daga harin, yayin da wasu da dama suka samu raunuka sakamakon harbin bindiga.

Bayan farmakar ƙauyen, maharan sun tare wasu motocin matafiya a kan hanya tare da yin awon gaba da ƙarin mutane kafin su tsere zuwa cikin daji.

Sarkin gargajiyar yankin, Oba Sunday Omodamori, ya tabbatar da aukuwar lamarin, yana mai cewa maharan sun zo da yawa kuma sun bazu a sassa daban-daban na al’umma kafin su fara kai harin.

Da take tabbatar aukuwar lamarin, Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Afusat Oyiza Saliu, ta ce jimillar mutane 30 ne aka sace da suak haɗa da maza 30 da mata huɗu. Ta ce, tuni dai rundunar ta fara ƙoƙarin ganin ta ceto waɗanda aka yi awon-gaba da su.

By Babaji

Leave a Reply