An sako ɗalibai 30 da malamai biyu na Kwalejin Yauri

Daga JAMIL GULMA a Kebbi

Rahotanni daga Jihar Kebbi na bayyana cewa, ɗalibai 30 da kuma  malamai biyu da aka sace daga makarantar Kwalejin Tarayya ta Birnin Yauri sun samu kansu.

Kamar yadda wata takarda mai ɗauke da sa hannun Alhaji Yahaya Sarki, Mataimaki na Musamman kan Harkar Yaɗa Labarai ga Gwamna Atiku Bagudu na jihar, ta bayyana cewa, “Yau Alhamis 21 (jiya) ga watan Oktoba, ɗalibai 30 daga makarantar FGC Birnin Yauri sun iso nan babban birnin jiha  bayan da aka sako su.

Yanzu haka ana cigaba da duba lafiyarsu kafin a sada su da iyayensu. Haka-zalika yanzu haka gwamnati tana nan tana iya ƙoƙarinta na ganin an sako sauran ɗalibai da malaman da ke hannun ’yan bindigar.”

Wakilin Manhaja ya zanta da Malam Ibrahim Abdullahi Gulma, ɗaya daga cikin ’yan uwan Malam Mukhtari Abdullahi Gulma, Mataimakin Shugaban Kwalejin Tarayya ta Birnin Yauri, dangane da sako ɗaliban, inda ya bayyana cewa, sun sami labarin sako ɗalibai 30 da malamai biyu, amma dai ɗan uwansu ba ya ciki, sai dai suna cigaba da addu’ar Allah ya fitar da shi tare da sauran duk waɗanda ke hannun waɗannan mutanen.

Malama Aina’u Yauri, uwar yara biyu ce daga cikin ɗaliban, ta bayyana wa wakilinmu cewa, ta sami labarin an sako waɗansu yara, amma dai har yanzu ba a kira su ba, don su je su ga ko da ’ya’yansu a ciki.

Ta ƙara da cewa, ita gaskiya daga farko ita ta ɗauki abin kamar almara, saboda ko satin da ya gabata sun sami labarin sako yaran, amma bayan da suka isa Birnin Kebbi, sai suka tarar maganar banza ce, wanda har ya yi sanadiyyar rasuwar wata mata a garin Koko da ke da ɗa  ɗaya kacal kuma yana cikin ɗaliban.

Sai dai an ɗauki tsattsauran matakai wajen hana ’yan jarida da sauran mutane zuwa kusa da yaran tun da aka shigo da su gidan gwamanti har zuwa lokacin da aka sake fita da su zuwa sansanin ’yan gudun hijira da ke Birnin Kebbi.

Tun ranar Laraba dai aka soma samun bayani kan sako waɗannan ɗaliban da malamai. Waɗansu bayanai da suke cin karo da juna sun bayyana wa  Manhaja cewa, ɗalibai 38, waɗanda suka haɗa da maza 36 da mata biyu da kuma malamai biyu, a ka sako, amma kuma wasu bayanan sun nuna cewa, ɗalibai 30 ne, kafin sanarwar gwamnatin.