An sako kwamishinan da aka yi garkuwa da shi a Neja

Bayan kwanaki biyar da yin garkuwa da shi, ‘yan bindiga sun sako Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Neja, Alhaji Sani Idris, da suka sace a jihar.

Sanarwar da ta fito daga ahalin kwamishinan, ta nuna an sako Idris ne da misalin ƙarfe 9:30 na dare ran Alhamis da ta gabata.

Mr. Ado Ada, wanda ɗan’uwa ne ga kwamishinan, ya bayyana farin cikinsu dangane da dawowar Idris, tare da danganta nasarar dawowar da ƙoƙarin ‘yan’uwansa ba tare da biyan wani kuɗin fansa ba.

Sanarwar ta ce bayan da aka sako Idris, sai da aka binciki lafiyarsa kana daga bisani aka miƙa shi ga ahalinsa.

‘Yan’uwan Kwamishinan sun nuna godiyarsu ga ɗaukacin jama’a dangane da irin goyon bayan da aka nuna musu a lokacin da Idris ya shiga hannun ‘yan bindigar.

Idan dai za a iya tunawa, an yi garkuwa da Idris ne a ranar Lahadin da ta gabata, inda wasu ‘yan bindigar da ba a san ko su wane ne ba suka sace shi da misalin ƙarfe 11 na dare a ƙauyen Babban Tunga da ke yankin ƙaramar hukumar Tafa.