An sako Sarkin Kajuru

Daga ABBA MUHAMMAD, a Kaduna

Bayanai daga jihar Kaduna sun nuna Sarkin Kajuru, Alhaji Alhassan Adamu, ya samu ‘yanci bayan sako shi da ‘yan bindigar da suka yi garkuwa da shi suka yi.

Babban ɗan Sarkin kuma Madakin Kajuru, Alhaji Musa Alhassan Adamu, shi ne ya tabbatar da labarin sakin sarkin.

Ya ce suna zaune a gida da rana, kwatsam sai suka ga sarkin ya shigo.

Sai dai ya ce ba a sako ragowar mutum 13 da aka yi garkuwa da su tare da sarkin ba.

Ya ce cikin ƙoshin lafiya mahaifin nasu ya komo gida. Amma cewa an garzaya da shi asibiti don duba lafiyarsa.

Ya zuwa haɗa wannan labari, babu wani rahoto a kan sai da aka biya kuɗin fansa kafin aka sako sarkin ko kuwa a’a.

Tun farko, ɓarayin sun buƙaci a biya su fansar milyan N200 kafin su sako sarkin, kamar dai yadda mai magana da yawun masarautar, Malam Dahiru Abubakar ya bayyana.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *