An samu hare-haren bom 1,934 a Arewa cikin shekaru bakwai – Bincike

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Rahotanni sun nuna cewa yankin Arewa maso Gabashin Nijeriya na ci gaba da fuskantar babbar barazana daga hare-haren bom, inda aka rubuta jimillar hare-hare 1,934 tsakanin shekarar 2017 zuwa 2024.

Binciken da aka fitar a cikin rahoton ‘2025 Nigeria Mine Action Reɓiew’ ya bayyana cewa mafi yawan hare-haren sun kasance ne ta hanyar dasa bama-bamai a kan hanyoyi, wato IEDs, wanda ya zama ruwan dare fiye da sauran hanyoyin kai hari.

A cewar rahoton, irin waɗannan bama-bamai na kan hanyoyi sun kasance mafi hatsari kuma mafi yawan faruwa a tsawon shekaru bakwai da aka nazarta, abin da ke nuna yadda ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya ke ci gaba da sauya dabarunsu.

Shekarar 2017 ce ta fi kowacce yawan hare-hare, inda aka samu kimanin 381. Sai dai daga bisani an samu raguwa a wasu shekarun kamar 2018 da 2019. Duk da haka, daga shekarar 2020 an sake ganin ƙaruwar hare-haren, lamarin da ya ci gaba har zuwa shekarun baya-bayan nan.

A shekarun 2023 da 2024 ma, an sake samun hare-hare 191 a kowace shekara, abin da ke nuna cewa duk da ƙoƙarin da ake yi na daƙile su, barazanar na nan daram.

Masana tsaro na cewa irin waɗannan hare-hare na IED suna zaya daga cikin manyan ƙalubalen da jami’an tsaro ke fuskanta, musamman a yankunan da ke fama da rikicin ‘yan ta’adda.

Shugaban Cibiyar Yaƙi da Ta’addanci ta ƙasa, Adamu Laka, ya bayyana cewa ‘yan ta’adda na ci gaba da ƙirƙirar sabbin hanyoyin tada bama-bamai, wanda ke sa su zama masu haɗari fiye da da.

Ya ce, tun daga shekarun baya, an ga yadda dabarun tayar da bama-bamai suka rikiɗe daga amfani da waya ko wayar hannu zuwa amfani da na’urorin da ke tashi idan an taka su, kuma yanzu ma ana ƙara inganta su.

A cewarsa, duk lokacin da jami’an tsaro suka gano wata hanya ta daƙile su, sai ‘yan ta’addan su ɓullo da wata sabuwar dabara, lamarin da ke ƙara tsananta matsalar tsaro.

Rahotanni sun ƙara jaddada cewa waɗannan hare-hare na jefa rayuwar fararen hula, jami’an tsaro da kuma muhimman ababen more rayuwa cikin haɗari.

Duk da matakan da gwamnati ke ɗauka, har yanzu ana buƙatar ƙarin haɗin gwiwa, fasaha da kuma tsauraran matakan tsaro domin kawo ƙarshen wannan barazana da ke ci gaba da addabar yankin.

By ukarofi