An samu sauƙin rashin tsaro a Nijeriya yanzu sama da lokacin Buhari, inji Ribaɗu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Mai bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkar Tsaro, Nuhu Ribaɗu, ya ce an samu sauƙin hare-haren ƴan ta’adda a faɗin Nijeriya ƙarƙashin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu akan na zamanin marigayi tsohon shugaba Muhammadu Buhari.

Da ya ke magana a taron ƙara wa juna sani da Gidauniyar Sir Ahmadu Bello ta shirya a Arewa House dake Kaduna, Ribaɗu ya ce atisayen sirri da dabarun jami’an tsaro a ƙarƙashin Tinubu sun samar da gagarumar nasara a faɗa da ta’addanci a ƙasar.

“A shekaru biyu da suka gabata, an halaka sama da sanannun jagororin ƴan ta’adda guda 300 kuma an ceto waɗanda aka yi garkuwa da su guda 12,100, sannan an ƙwato haramtattun makamai sama da 14,000 da lalata su”, inji Ribaɗu.

Ya bayyana cewa, ayyukan daƙile ta’addanci a yankin Arewa ta Yamma na sojoji ya taimaka wajen ceto mutane 11,259 da aka yi garkuwa da su zuwa wata Mayu, 2025, sannan an kashe sanannun ƴan bindiga da dama gami da tarwatsa dabobinsu a Jihohin Zamfara, Kaduna da Katsina.

Ribaɗu ya kuma yaba wa Gwamnan Kaduna, Uba Sani bisa amfani da hikimomi wajen magance matsalolin ta’addanci a yankunan Kaduna ta Kudu, Birnin Gwari da wasu sassan jihar, yana mai cewa hakan abu ne da ya cancanci yabo duba da tasirinsa acikin al’umma.

“Kaduna yanzu kaso 80 ta samu tsaro saboda gwamnatin jihar tana aiki hannu da hannu da mu”, inji shi.

By Babaji