Abin da ya sa na shirya kasuwar Bajekolin littattafai – Kabiru Jammaje

Spread the love

DAGA MUKHTAR YAKUBU

A ranar 27 ga Yunin da ya gabata ne aka ci kasuwar rana guda ta Bajekolin littattafai ko gwanjo littafai, wanda fitaccen malamin Turanci Malam Kabiru Musa Jammaje ya shirya wanda dunbun jama’a malamai da kuma ɗaliban ilimi suka halarci wajen bajekolin littattafan domin sayen littattafan wanda aka sayar da su cikin farashi mai sauƙi.

Wani abin burgewa kasuwar Bajekolin littattafan ta tsawon wuni guda ce da aka shirya za a bajekolin littattafai sama da 450 domin sayarwa ga masu buƙata. 

To sai dai kasuwar ta ci ta cinye a ƙasa da sa’o’i uku na fara bajekolin, inda mutane daga ciki da wajen Kano suka yi taron cikar kwari a wajen bajekolin da ke tsohon ofishin Jammaje na Shatale talenTal’udu suka saye littattafan.

Bayan kasuwar bajekolin ta ci ta watse ne wakilinmu ya nemi jin ta bakin Malam Kabiru Musa Jammaje a game da manufar shirya taron bajekolin.

Malam Kabiru Musa Jammaje ya ce, “To shi dai wannan taron na bajekolin ko gwanjon littattafai da na shirya, idan za ka iya tunawa a kwanakin baya an yi wata muhawara tsakanin Farfesa I B K da Dakta Bala Muhammad, a kan maganar karance-karance ko a jikin allo ko ta hanyar littattafai. 

To wannan muhawara da aka yi ta fitar da saƙo mai ƙarfi ga al’umma na cewa ya zama dole a tashi a rungumi karance-karance. Kuma bayan da aka yi wannan muhawara ne na samu wani ilimi na kwaso littattafai na da na yi amfani da su na yi gwanjon su ta hanyar bajekolin su, kuma na sayar da su cikin farashi domin su ma al’umma su amfana.

Kuma su waɗannan littattafai ne da na rinƙa tattarawa a ƙasashen waje na sayo su da yawa na karanta su. Don haka na ga bai kamata na yi ta ajiyar su ba, kuma ga masu buƙata suna nema. Duk da cewar wannan littattafan ba su fi kashi 30 cikin 100 na littattafai da nake da su ba, na dai kwaso kaɗan ne daga ciki.”

Da yawa akwai waɗanda suka yi tunanin ko littattafan da ka wallafa ne za ka yi bajekolin su sai kuma aka ga wasu ne daban.

Ai daman kamar yadda muka sanar musamman a soshiyal midiya mun faɗi cewa littattafai na cikin gida da na ƙasashen waje. To ka ga tun da na ce har da na ƙasashen waje bai kamata mutane su ɗauka cewar littattafai na ba ne kawai. Don a cikin littattafan da aka yi gwanjon su wanda na wallafa biyu ne ko uku. Kuma dai ka ga littattafan da aka kawo sun kai sama da 460, kuma kusan dukkan su na ƙasashen waje ne, don haka da yawa mutane sun san cewa ba littattafai ne da na rubuta ba, kamar dai yadda na ɗauki hoton su na nuna a soshiyal midiya, don haka mutane sun san me za su gani.

A sanarwar dai an nuna za a yi bajekolin daga sha biyu zuwa bakwai na yamma, sai kuma kasuwar ta ci ta ƙare a ƙasa da sa’o’i uku aka kammala.

To ni ma dai abin da ya ba ni mamaki kenan, don mun shirya za a kai yamma ɗin, amma sai ya zamana an fara sha biyu, amma a cikin minti 30 aka saye kusan rabin littattafan don haka sai ya zama ba za mu kai yamma ɗin ba saboda kaso 90 cikin 100 na littattafan sun ware. Kuma gaskiya na ji daɗi sosai da jama’a suka amsa kiran, kuma babu abin da zan ce wa mutane musamman abokaina na Facebook sai godiya. Tun da a Facebook ne na tallata taron bajekolin kuma mutane suka taya ne jama’a suka gani suka zo suka sai saya, wanda hakan ya nuna suna son karance-karance, suna son ilimi, kuma suna son su ci nasara a rayuwa. Kuma Alhamdulillah mu kan mu mun cimma nasarar abin da muka tsara na shirya kasuwar bajekolin.

Ko akwai wani lokaci nan gaba da ake tunanin za a ƙara yi tun da an samu nasara?

To gaskiya ba zan iya cewa ga lokacin da za a ƙara yi ba, saboda wannan littattafai ne da aka daɗe ana tara su, don wasu na sayo su a Indiya wasu a Afirka ta Kudu wasu a Kenya da Ingila, duk ga su nan dai littattafai ne kala-kala da aka daɗe ana tara su, don wasu za ka ga na saye su tun 2010 zuwa yanzu, don haka babu wata ranar da za ka ce za ka ƙara yi sai dai idan lokaci ya bayar da a kara yi.

Su waɗannan littattafai da yawa masu sayen su sun shaida mana sun daɗe suna neman su ba su samu ba a kasuwanni, ko yanayin farashin ya yi sauƙi kenan?

Wato daman abin da na yi duba da shi kenan. Na farko dai su littattafan nan masu kyau ne na asali ba kwafi ba, na samo su ne daga kamfanonin da suka buga su. Sannan kuma ba littattafai ne da za ka iya samun su a kasuwar mu nan kai tsaye ba, don haka sai suka kasance cikin sauƙi kuma za ka same su ba tare da ka sha wahala ba, don mafi yawan su sai ka je ƙasashen waje za ka iya samun su, don haka ka ji ko wanɗanda suka zo saya ɗin abin da suke ta faɗa kenan. Sai ka ji wani ya ce ya yi shekaru yana nema bai samu ba. Kuma littattafan da za ka saya dubu biyar a nan, idan a kasuwa ne sai dai ka yi maganar dubu ashirin, don mun yi sauƙi ne na kashi hamshin cikin ɗari ko ma sama da hakan, don babu littattafai da ya wuce dubu biyar a cikin waɗanda muka sayar, don haka wani sauƙin da muka yi ya kai na kashi tamanin cikin dari. Don haka ina kara godiya ga dukkan Jama’ar da suka halarci taron Bajekolin da Dalibai na da sauran jama’ar da suka zo don mutane da yawa na daɗe ban gan su ba sai a wannan lokacin, don haka wannan bajekolin ya zama kamar wani taron sada zumunci tsakani na da masoya da ɗalibai na musamman tsofaffin da suka kammala makarntar Jammaje Actually a baya, sun nuna mana su ‘yan halak ne sun yi mana kara sun zo da yawa.

Ina godiya sosai Allah ya saka da alheri, Allah ya bar zumunci.

To Madalla mun gode.

Ni ma na gode sosai.

By ukarofi