An sayar da tsohon wando kan Naira Miliyan 50

Wani mutumi ya lale maƙuden kuɗaɗe har Naira miliyan 50.78 ya saya wani wandon jins ɗin da aka zaƙulo a kasan teku.

Wani wandon maza wanda aka gano ya kasance mafi tsufa da daɗewa kuma an yi gwanjonsa kan Dala 114,000 wanda ya yi daidai da Naira miliyan 50.7.

Farin wandon an tsamo shi ne daga wani jirgin ruwa da ya nitse tun a shekarar 1857 a Arewacin Carolina.

A yayin jawabi kan nasarar da aka samu wurin sayar da shi, Dake Dwight Manley, Manajan California Gold Marketing Group ya ce, “haƙo wannan wando da masu haƙo ma’adanai suka samu nasarar yi, sun kafa tarihi sosai. Domin kuwa babu irin wandon yanzu kwata-kwata a duniya.”

Jirgin ruwan ya nitse a watan Satumban shekarar 1857 inda mutum 425 suka mutu daga cikin fasinjoji 578 da matuƙan da ya ɗauko. A lokacin wannan labari ya ɗimauta duniya sosai.

Fasinjojin na ɗauke da tan 21 na sulalla da gumaka yayin da jirgin ruwan ya nitse. An gano hakan ne a karo ba farko a shekarar 1988.

Wani mutumi daga Oregon, wanda ya saye su a San Francisco ne ya zuba Kuɗi ya kwashe, cewar kamfanin gwanjon.

Jami’an gwanjon sun ce wandon mai botura biyar ya nuna ƙirƙira ta farko da Leɓi Strauss suka fara sayarwa na kaya a ƙarni na 17. Wando mai daɗaɗɗen tahiri.