
Daga BELLO A. BABAJI
Tsohon Babban Sakataren Hukumar Inshora ta Ƙasa (NHIS), Farfesa Usman Yusuf ya musanta laifuka biyar da aka tuhume shi a kai, waɗanda suke da alaƙa da badaƙala.
A ranar Litinin ne Hukumar EFCC ta gurfanar da farfesan a Babban Kotun Tarayya dake Abuja, bayan kama shi a ranar Laraba bisa zargin yin amfani da damammakin ofishinsa wajen amfanar da kansa daga shekarar 2016 zuwa 2017.
EFCC ta zarge shi ne da amincewa da sayen abun hawa da aka yi wa kasafin N30m akan Naira miliyan 49.19.
Ta kuma zarge shi da bada kwangilar N10m ga Gidauniyar GK Kanki ga horar da mutane 90 da aka yi ba bisa ƙa’ida ba.
A lokacin da ya ke magana, Farfesan ya musanta baki ɗaya abubuwan da aka zarge shi a kansu.
Daga nan sai Mai Shari’a Nwecheonwu ya ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 12 ga watan Fabrairu tare da bada umarnin a tsare shi a gidan gyaran hali na Kuje a yayin da ake jiran neman bada belinsa.
