
Daga BELLO A. BABAJI
Wata Babbar Kotun Tarayya dake Lokoja Jihar Kogi, ta tsige Ohinoyi na Masarautar Ibira (Ohinoyi of Ebiralanad), Mai Martaba Ahmed Muhammed Tajani Anaje daga muƙaminsa.
Mai Shari’a Salisu Usman, wanda ya yi hukuncin a ranar Litinin, ya umarci tuɓaɓɓen Sarkin da ya daina gabatar da kansa a matsayin Sarki daga yanzu.
Hakan na zuwa ne a lokacin da wani Dakta Barnabas Adeku Ojiah da wasu mutane biyu da ke adawa da gwamnan jihar suka shigar da ƙara.
