An tsaurara tsaro a Majalisar Dokokin Nijeriya yayin da mambobi ke zaman gaggawa

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

A yayin da ake shirye-shiryen fara zanga-zangar tsadar rayuwa a faɗin Nijeriya, ƴan majalisar dokoki suna gudanar da zama na gaggawa zauren Majalisar.

Sakamakon haka ne aka tsaurara matakan tsaro a kewayen Majalisar, biyo bayan zargin zanga-zanga ka iya ɓarkewa da za ka iya haifar da dakatar da zaman.

A ranar Lahadi ne ƴan Majalisar Dokokin su ka sanar da batun wanda hakan ya shafi kwanaki hutunsu na shekara da su ka fara a makonnin da su ka gabata.

Wata sanarwa da mai magana da yawun ƴan majalisar wakilai, Rotimi Akin ya fitar ta ce, zaman ya ƙunshi manyan batutuwan gaggawa da su ka shafi al’ummar Nijeriya.

Akin ya ƙara da cewa, haka ba baƙon abu ba ne idan aka ga wani al’amari da ya shafi ƙasa ya taso a ga Majalisar ta tsayu a kan samar masa da mafita.

By Babaji