
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Gwamnatin Jihar Katsina ta umarci a rufe dukkan makarantu a faɗin jihar.
Sanarwar ta fito daga mai magana da yawun ma’aikatar ilimin ƙananan makarantu, Ɗanjuma Sulaiman inda ya ce gwamnatin ta ce a sanar da mutane musamman iyayen yara cewa hutun zai fara ne daga ranar Laraba.
Ya ƙara da cewa, hutun shi ne mafarin hutun zango na uku, ɗaya daga cikin zango-zango da makarantun ke yi a shekarar.
Ya yi kira ga iyayen da su ɗakko ƴaƴansu da ke karatu a makarantun kwana zuwa gidajensu, ya na mai cewa dokar ta shafi makarantun kuɗi da na gwamnati a faɗin Jihar baki ɗaya.
