An wulaƙanta min littafi na wai don ni yaro ne – Aliyu Idris Author

*Marubuci kan sauya gurɓatattun tunanin mutane zuwa nagartattu – Aliyu Idris Author

A lokacin da a ka ga littafi, hankali da tunanin mai karantawa zai tsaya akan babban mutum ne ya rubuta shi, wato mai yawan shekaru. Har ta kai idan a ka ga marubuci da ƙarancin shekaru sai a rena rubutun sa tun kan a karanta. Hakan ce ta sa yara ma su sha’awar rubutu jikin su kan yi sanyi idan sun tuna yanda a ke wa marubuta tsaran su. Dalilin ke nan da yasa ba kasafai ake samun marubuta masu ƙananen shekaru ba, duk da cewa akwai masu baiwar da idan an ba su dama za su iya taka rawar ganin a duniyar rubutu. Wannan karon manhaja dai ta taɓo ɗaya daga cikin marubuta da su ka faro a ƙurciya. Don jin yadda tattaunawar ta kasance, sai ku gyara zama:

Daga AISHA ASAS

Mu fara da jin tarihin ka.
Da farko Sunana Aliyu Idris Author (Sarkin Yaƙin Malumman Matazu). An haifini a garin Zarena da ke Ƙaramar Hukumar Birinin kudu, a Jahar Jigawa, Nijeriya. Ranar ɗaya ga watan Oktoba na shekarar miladiyyya ta 1994. Na fara yin karatun Fiƙihu da na Alƙur’ani a wajen Malamina Malam Sa’idu Muhammad, da ya ke a garin Zarena. Duk lokacin dana samu hutun makaranta sai na tafi Kano domin ƙarin neman ilimin Addini.

Na fara karatun firamare a garin Zarena daga 1999-2005 dana Jiniyo daga 2005-2008. Bayan da na gama sai na tafi Sakandaren Kwalejin ilimi ta gwamnati da ke Birinin Kudu daga 2008-2011, bayan da na kammala karatuna na samu matsalar gyaran Jarrabawa sai na sake koma wa Makarantar Sakandaren Gwamnati da take a Maigatari daga 2012-2014. Alhamdu lillahi na samu sakamakon mai kyau a wannan lokacin. Bayan nan na fara karatun gaba da Sakandare a matakin pree N.C.E, da na gama kuma na samu nasarar shiga matakin N.C.E. Inda na karanci fannin Turanci da Tarihi a Kwalejin Llimi ta Gumel da ke Jahar Jigawa daga 2015-2018. Yanzu haka kuma ina kan yin karatuna na digiri a fannin Turanci a Kwalejin Ilimi ta Gumel reshen Jami’ar Bayero da ke kano. Ni Marubuci kuma Mawaƙi, ina rubutun littattafan Hausa da na Turanci da kuma sauran rubutattun waƙoƙin Hausa. Bayan haka kuma ina yin sana’ar sai da littattafai a kasuwa a yanzu haka.

Wace shekara ka fara rubutu?
A shekarar 2018 na fara yin rubutu gaskiya, kuma har yanzu ina kan yinsa cikin Ikon Allah.

Ko za mu iya sanin littafan ka.
Eh akwai littattafaina da dama waɗanda na rubuta su kamar haka: Knowledge Is Power’, Knowledge Is Foundation’, Ilimi Jigon Rayuwa’, littafin waƙa mai suna Ilimi Dukiya, da sauran waɗanda ban fitar da su ba. Akwai kuma rubutattun waƙoƙi su ma sun kai kimanin guda 100 da na rubuta.

Wane ne za a iya kira da Marubuci?
Marubuci shi ne wanda yake ƙirƙira ya wallafa sabon rubutu, ya kuma yi amfani da fasaharsa domin ilimantar da al’ummarsa.
Murubuci shi ne fitilar al’ummar a ko da yaushe, domin shi ne wanda yake haskaka wa al’ummarsa zuwa hanyar da ya kamata su bi domin inganta rayuwarsu.
Marubuci ya na warwarewa da samar wa mutane mafita zuwa hanyar ɓullewa game da wani abin da ya ke damunsu wata ƙila ma ya zama wutar daji ko ruwan dare a cikin al’umma da taimakon fasaharsa da bincike har a samu mafita.


Marubuci shi ne yake faɗakar da mutane wani ilimin rayuwa da ba su da sani ba, wanda zai iya gyara zamantakewarsu da iyali, ‘yan’uwa, abokai da mu’amalolin rayuwarsu da jama’a. Sannan kuma Marubuci ya inganta rayuwar al’umma domin samun ci gabansu mai ɗorewa.
Marubuci kan sauya gurɓatattun tunanin mutane zuwa nagartattu. Misali: Sauya tunanin shiga ta’addanci a gane daɗin zaman lafiya da ribar da ya ke haifarwa, kawar da tunanin shaye-shaye da illarsa ga lafiya. Bayan haka, Marubuci ya na cusa wa mutane ilimin zamani cikin hikima a rubutu su waye su ciyar da rayuwarsu gaba.


Haka zalika, Marubuci shi ne yake zaƙulo abubuwan da mutane ba su san su ba, ba su taɓa ganinsa ba, wata mila ma ba su ma taɓa jin labarinsa ba. Ka ga a nan, Marubuci ya na cusa basira da yaye duhun kai a ƙwaƙwalen mutane.

Ko za mu iya sanin littafan ka da su ka shiga kasuwa?
Littafina wadda ya shiga kasuwa shi ne Knowledge Is Power. A yanzu haka a na siyar da shi a kasuwa, kuma Alhamdu lillahi ya samu karɓuwa ga ɗalibai domin ilimin da ke cikinsa ya na mutuƙar amfani ga rayuwar al’umma.
A marubuta ka na da uwa/uban gida?
A marubuta ban isa na ce bani da Uwa/Uban gida ba, abin alfahari ne a ce kana da Jagora a ko meye na rayuwa, shi ne zai taimakama ya kuma nuna maka dabarun koyon rubutu da kuma ɗora ka a kan hanyar da ta da ce, har ka kai wata rana kai ma ka zamo zakara. Ni dai a gurina Uwa/ Uban gida a fagen rubutu shi ne duk wanda zai gyara maka rubutunka, ko kuma ya baka shawara mai kyau shi ne Uban gida na gari mai ƙaunarka a waje na.

Me ka ke fatan cimma a harkar rubutu?
Babban burina a harkar a rubutu shi ne, na bada gudunmawata a fannin ilimi, domin samun gyara da kawo ci gaban tarbiyyar al’ummar ƙasata da sauran ƙasashen duniya ga bakiɗaya. Wannan shi ne babban burina , kuma a ko da yaushe ina ta addu’ar Ubangijinmu ya bani Ikon yin hakan amin.

Wane lokaci ka fi sha’awar yin rubutu?
Ni gaskiya na fi sha’awar yin rubutu a duk lokacin da abin da zan rubuta ya zo min , to a dai-dai wannan lokaci ne sai na ji sha’awar yin rubutu ta zo min, sai kawai na ɗauki alƙalamina.

Ko akwai wani abu da ba za ka manta da shi ba a cikin duniyar rubutu?
Akwai wani abu da ba zan taɓa manta ba a duniyar rubutu, wannan abu shi ne, akwai wani lokaci da wani mutum shi da matarsa za su rubuta littafi mai suna ‘A Tallafa Wa Marayu’ su ka zo su ka same ni har gida na ba su shawarwari da kuma yi musu gyare-gyare a kan littafin tun daga farko har zuwa ƙarshe, a taƙaice ma ni ne wanda na kai su har zuwa wajen kamfanin da zai yi musu aikin buga littafin, kuma ina ɗaya daga cikin mutanen da na taimaka musu a wajen ƙaddamar da littafin. Amma daga ƙarshe sakamakon da su kai min shi ne ƙara ta a wajen ‘yan sanda a ka tafi da ni, saboda ba sa so su biyani haƙƙina. Gaskiya ba zan taɓa mantawa da lokacin ba a rayuwata.

Lokacin da ka fara rubutu, ka nemi shawarwari daga waɗanda su ka fara kafin ka?
A lokaci da na fara rubutu shi ne na je koyon koyarwa (Teaching pratice) a nan ne na fara yin rubutu sosai, sai bayan da na gama rubuta littafin farko “Knowlege Is Power” sannan na nemi shawarwari daga malamaina, amma a cikin duk malaman da na kai wa gyaran littafin malami ɗaya ne ya ba ni kulawa ta musamman a wajen gyaran littafin nawa. Wannan malamin ba zan taɓa mantawa da shi ba a rayuwa, saboda goyon bayan da ya ba ni a lokacin da nake ƙoƙarin yin rubutun, wato Dr. A.O Adedokun (JSCOE GUMEL) kenan.

Ka fuskanci wasu ƙalubale?
Babban ƙalubalen da na taɓa fuskanta shi ne, ƙarata da akai a harkar rubutu har ma aka tafi da ni a wajen ‘yan Sanda, akwai kuma matsaloli na tafiye-tafiye wanda dole suna buƙatar kuɗi. Bayan haka akwai wata akuyata saboda harkar rubutu sai da na sayar da ita sakamakon rashin kuɗi. Amma yanzu Alhamdu lillahi mun gode wa Allah, kwalliya ta biya kuɗin sabulu.

Nasarori fa?
Na samu nasarori ƙwarai da gaske a harkar rubutu wadda sun wuce na lissafa su, amma ɗaya daga cikin irin nasar da na samu ita ce Sarautar Sarkin Yaƙin Malumman Matazu, samun shugabanci a cikin ƙungiyoyi da dama, ‘Award’ da na samu na lambar yabo da dama a fanni daban -daban, ana yin hira da ni a jaridu da gidajen radiyo da dama , da kuma buga littattafaina da yin amfani da su a fannoni da dama na rayuwa. Alhamdu lillahi na samu nasarori da yawa a rayuwa ta ko’ina, kuma har yanzu ina zaune da iyayena lafiya.

Ko akwai wani marubuci da ka ke burin ka taka matsayin da ya kai?
Kawai ni babban burina shi ne na ba da gudunmawata kamar yadda sauran ‘yan’uwana marubuta da suke bayarwa domin gyaran tarbiyyar al’umma, wannan shi ne kawai babban burina. Bayan haka kuma ina mutuƙar ƙaunar marubuta da mawama a rayuwata.

Ka fuskanci matsala ta ɓangaren siyar da littafin ka?
Eh, gakiya matsaloli basa ƙarewa a ko da yaushe a cikin rayuwa, akwai lokaci da na kai tallan littafina wata makaranata a Jahar Jigawa, Shugaban Makarantar gaskiya ya wulaƙanta min littafina, wai saboda ni yaro ne na yi gaggawar rubuta littafi a yanzu.

Wace shawara za ka ba wa marubuta ‘yan’uwan ka?
To ni a gaskiya shawarata da na ke so na ba wa ‘yan’uwa marubuta ita ce dole ne su zama masu yin binkice da ƙoƙari da nuna juriya a kan duk abin da su ka saka a gaba, domin samun nasar rayuwa. Dole marubuci ya dage da yin addu’a a kan abin da yasa gaba a ko da yaushe, marubuci ya zama mai haƙuri a kan komai, ya kuma cire son zuciyarsa da son kayan al’umma sai ya zauna da kowa lafiya. Marubuci ya na da kyau ya faɗi gaskiya a kan komai domin kawo zaman lafiya a cikin al’umma.

Mun gode da lokacin ka.
Ni ma na gode. Kuma ina nara nuna godiyata, da nuna yabawa ga irin gudunmawar wannan jarida ta MANHAJA ta ke bayarwa ga alumma domin bunƙasa Adabin Hausa da kuma marubuta a ko yaushe. Ubangiji Allah ya ƙara ɗaukakata a faɗin duniya, amin. Na gode sosai.