Gwamnatin Tarayya ta bada sanarwar cewa tana nan tana shirin ganin yadda za ta farlanta wa ma’aikatan gwamnati a faɗin ƙasa yin allurar rigakafin cutar korona.
Gwamnatin ta ce a hankali za ta gudanar da tsare-tsarenta don cimma ƙudurinta inda za ta tabbatar da cewa akwai wadatar allurar da kuma samun ta cikin sauƙi kafin ta kai ga ƙaddamar da shirin.
Sakataren Gwamnatin Tarayya kuma shugaban kwamitin Shugaban Ƙasa Kan Yaƙi da Cutar Korona, Boss Mustapha ne ya bayyana hakan a wajen taron kwamishinonin lafiya a Abuja.
Mustapha ya ce, “Tabbas lokacin farlanta yin rigakafin zai zo. Kafin wannan lokaci, muddin ba ka da katin shaidar rigakafin zazzaɓin maleriya, ba za a bari ka shiga wasu ƙasashe ba sai bayan da aka tsame Nijeriya daga jerin ƙasashen da ke fama da zazzaɓin.”
Don haka ya ce yanzu halin da ake ciki, duniya ta kama hanyar amfani da wannan tsari ta hana shiga ƙasashe ba tare da katin shaidar rigakafin korona ba.
Saboda a cewarsa, da zarar manyan ƙasashen duniya suka kammala yi wa mutanensu rigakafin annobar, daga nan babu wanda za a bari ya shiga ƙasashen ba tare da ya yi rigakafin korona ba.
Mustapha ya ce tuni an soma ganin irin haka a ƙasashen Turai, inda ake ɗaga wa waɗanda suka yi rigakafin ƙafa kan wasu al’amura, “Don haka, gara mu soma shirya jama’armu tun daga gida”, in ji shi.
A cewar Mustapha, “Ɗaya daga cikin dalilan da ya sa muke so mu soma shirin da ma’aikatan gwamnatin tarayya shi ne, saboda za su riƙa tafiye-tafiye zuwa ƙasashen duniya don aiwatar da wasu ayyuka a madadin Gwamnatin Najeriya.”
Don haka ya ce wannan al’amari ne mai matuƙar muhimmanci, wanda sannu a hankali gwamnati za ta riƙa yin ‘yan shirye-shiryenta don cimma buƙata.