Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed Abdulkadir, ya rantsar da Ibrahim Kashim Imam a matsayin Sakataren Gwamnatin Jihar (SSG) da Dr Aminu Gamawa a matsayin Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnatin Jihar da mataimakinsa Bashir Ya’u haɗa da kwamishinoni 21 da sauransu.
Babban Alƙalin Jihar, Justice Rabi Talatu Umar, ita ce ta jagoranci rantsar da jami’an a babban zauren taro da ke Fadar Gwamnatin Jihar a wannan Juma’ar.
Da yake jawabi yayin bikin rantsarwar, Gwamna Bala ya nusar da jami’an kan cewa gwamnati da ma al’ummar Bauchi baki ɗaya, na sa ran ganin aiki tuƙuru daga gare su.
Kazalika, gwamnan ya gargaɗe su da kada su nuna wa kowane ɗan jihar wariya ko bambanci da wannan sabon muƙamin da aka naɗa su, yana mai cewa kowane ɗan jihar na da ‘yanci a gwamnatinsa.