An yaba da yadda Hon. Kana Ahmad ke canja fasalin hukumar samar da ruwa a Jihar Nasarawa

Daga JOHN D. WADA a Lafiya

An yaba wa sabbin dabaru da sabon Janar Manajan Hukumar Samar da Ruwa na Gwamnatin Jihar Nasarawa, Honorabul Kana Ahmad Mohammed ke cigaba da ƙirƙirowa a yanzu don canja fasalin hukumar a jihar.

Injiniya Mohammed Addra wanda shine manajan daraktan babban cibiyar dake kula da harkokin ruwa a shiyar Arewa ta Tsakiya wato Lower Benue River Basin Authority (LBRBA) a turance ne ya bayyana haka a lokacin da janar manajan hukumar ta ruwa a jihar Nasarawa, Honorabul Kana Ahmad Mohammed ya jagoranci sauran shugabannin hukumar inda suka kai wa cibiyar ta LBRBA wata ziyarar aiki na musamman a ofishin cibiyar dake Makurdi a jihar Benuwai.

Injiniya Mohammed Addra ya ce bai yi mamakin ɗimbin nasarori da hukumar ruwa ta gwamnatin jihar Nasarawa ta ke samu a yanzu a ƙarƙashin jagorancin Kana Ahmad Mohammed ba don ya san shi da daɗewa a matsayin ƙwararre da ya san duka harkoki da suka shafi ruwa a jihar ta Nasarawa da ƙasa gaba ɗaya.

Ya ce ya tabbata al’ummar sun yi babban dace na samun Kana Ahmad Mohammed a muƙamin.

Ya kuma tabbatar wa bakin nasa cewa a shirye cibiyar sa take ta haxa hannu da hukumar don cimma burin kyakkyawar manufar hukumomin 2 musamman na samar da wadatattun ruwa da amfanin gona da kauce wa ambaliya da sauran su.

Tun farko a jawabin janar manajan hukumar samar da ruwa na jihar Nasarawa, Kana Ahmad Mohammed ya ce ziyarar na da matuƙar muhimmanci da tarihi kasancewa shine irin sa na farko da hukumar ta kai wa cibiyar ta LBRBA a Benuwai tun kafuwar ta.

Ya ce ziyarar ya zame wa hukumar dole a ƙoƙari da take yi na mai do da martaba da gudanar da harkokin hukumar yadda ya kamata.

A cewar Kana cibiyar ta LBRBA a matsayin ta na babbar cibiya dake kula da harkokin ruwa a shiyar wadda hukumar sa na Nasarawa ke ƙarƙashin ta, sun yanke shawarar ziyartar ta me don su gana su kuma nemi mafita ga ƙalubale da suke fuskanta a hukumomin 2 da suka haɗa da ambaliyar da wutar lantarki da tattara bayyanai da sauran su a shiyar.

Janar Manajan ya kuma yi amfani da damar inda ya sanar wa manajan daraktan cewa a yanzu jihar ta Nasarawa na fuskantar barazanar ambaliyar ruwa dake shafar wasu manya kuma muhimman gonakin gwamnati da suka haɗa da gonar shinkafa na Olam dake yankin karamar hukumar Doma da na rake na Ɗangote dake yankin Awe dukan su a jihar da sauran su inda ya buƙaci haɗin kai da shawarwari tsakanin hukumomin 2 akoyaushe don samun nasarori a harkokin ruwa a jihar da shiyar dama ƙasa gaba daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *