Batun maida Mohammed Dauda kan shugabancin hukumarmu ba gaskiya ba – NIA

Daga BASHIR ISAH

Hukumar Tattara Bayanan Sirri ta Ƙasa (NIA), ta ce, Kotun Ɗaukaka Ƙara ba ta maida Mohammed Dauda kan kujerar Darakta-Janar na hukumar ba kamar yadda wasu kafafen yaɗa labarai suka yaɗa.

Cikin sanarwar da ya fitar a Abuja, Shugaban sashen shari’a na hukumar, Mr A. H. Wakili, ya ce ba gaskiya ba ne cewar an dawo da Mohammed Dauda kan muƙamin shugabancin hukumar.

Sanarwar ta ce: “An ja hankalinmu kan wani rahoton da ba daidai ba wanda aka yaɗa a intanet dangane da maido da Ambasada Mohammed Dauda matsayin Darakta-Janar na Hukumar Tattara Bayanan Sirri ta Ƙasa (DGNIA) wanda Kotun Ɗaukaka Ƙara ta yankin Abuja ta yi.

“Yana da muhimmanci mu wayar da kai cewar, asali Mohammed Dauda ba tabbataccen Darakta-Janar na hukumar ba ne, an dai naɗa shi ne na wucin-gadi bayan ƙarewar wa’adin Ambasada Ayo Oke, CFR, bayan kuma Ambasada Arab Yadam ya yi riƙon ƙwarya na ɗan lokaci, har sai da Shugaba Muhammadu Buhari ya naɗa Ambasada Ahmed Rufai Abubakar, CFR a matsayin tabbatacce Darakta-Janar.”

Sanarwar ta ƙara da cewa, “Al’amarin da Kotun Ma’aikata ta Ƙasa da Kotun Ɗaukaka Ƙara suka yanke hukunci dangane da korar Mohammed Dauda a matsayin Daraktan NIA bisa wasu laifuffuka da keta haddi.

“Batun ɗaukaka ƙarar da aka yanke masa hukunci na da alaƙa ne kawai da al’amuran da suka shafi korar. Har yanzu ana kan shari’a game da laifuffukan da ya aikata don yanke hukunci.

“A bayyane yake cewa labarin ƙaryar da aka yaɗa shiryayyen al’amari ne a tsakanin Ambasada Mohammed Dauda da muƙarrabansa domin kawar da hankalin jama’a,” in ji sanarwar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *