An yaba wa gwamnati da jami’an tsaro a Filato bisa shagulgulan sallah cikin lumana

Spread the love

Daga HABU ƊAN SARKI, Jos

An yabawa gwamnatin Jihar Filato da gamayyar haɗin gwiwar jami’an tsaro dangane da zaman lafiyar da aka samu a cikin garin Jos da kewaye yayin shagulgulan Sallah babba da aka gudanar.

Wakilin gwamnan jihar Caleb Mutfwang a yankin Arewacin Jos ta Arewa, Honarabul Nuru Shehu shi ne ya yi wannan yabon, tare da jinjinawa haɗin kan da shugabannin al’umma suke bayarwa, don cigaban zaman lafiya da haɗin kan al’ummar Filato.

Ya ce, an jima ba a gudanar da shagulgulan Sallah cikin kwanciyar hankali da lumana ba, kamar a wannan shekara, sakamakon jajircewa da gwamnati a matakin ƙaramar hukuma da na jiha, da masu faɗa a ji, domin ganin an yaƙi gungun matasa ýan daba, da ke tayar da zaune tsaye a lokacin sallah, suna sare-sare da wuƙaƙe da jikkata mutanen da basu ji ba, basu gani ba. A dalilin haka wani lokaci har da asarar rayuka ake samu.

“Na ji daɗi sosai da na ga har waɗanda ba musulmi ba ma sun fito, domin taya ýan’uwa musulmi murna da bikin babbar Sallah, wanda a shekarun baya ba a cika samun hakan ba, saboda ƙalubalen tsaro da ake fuskanta a Jihar Filato. Yanzu an samu galaba kan masu kawo fitintinu da rikice-rikice, don hana jama’a rayuwa cikin sukuni da karkatar da hankalin gwamnati.”

“Ina fatan manyan gari da sauran masu faɗa a ji za su cigaba da bai wa gwamnati da jami’an tsaro haɗin kai, tare da tsawatarwa matasa don su zama mutanen kirki, su daina shaye-shaye da ɗaukar makami suna cutar da rayuwar su, a matsayin su na jigon kowacce al’umma.”

Ya ƙara da cewa, bai kamata ana ce wa matasa manyan gobe ba, kasancewar kuwa su ne ginshiƙin cigaban kowacce al’umma, su ne ya kamata a riƙa sanyawa a gaba ana nuna musu yadda shugabanci yake tare da shawarwarin magabata.

“Ina ganin bai dace a ce matashin da ya san abin da yake yi zai tsaya yana biye wa lalatattun abokai da ɓatagarin ýan siyasa, suna ɓata masa rayuwa da nisanta shi daga kyakkyawar rayuwar da take jiran sa ba.”

By ukarofi