Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Wata kotu ta musamman ta yanke wa Aung San Suu Kyi, tsohuwar shugaban ƙasar Myanmar hukuncin ɗaurin shekaru huɗu a gidan yari.
An same ta da laifukan hure wa mutane kunne su yi bore da kuma karya dokokin daƙile yaɗuwar annobar Korona a ƙasar.
Suu Kyi ta kasance a tsare tun bayan da sojojin ƙasar suka tuntsure da gwamnatin farar hula a ranar 1 ga watan Fabrairu.
Juyin mulkin na zuwa ne shekaru 10 bayan da sojojin suka miƙa wa farar hula mulki a ƙasar.
Myanmar ta kasance a ƙarƙashin mulkin sojoji har sai da aka fara samun sauye-sauyen dimokraɗiyya a shekarar 2011.
Suu Kyi ta musanta zargin da aka ma ta.
Tsohuwar shugaban tana fuskantar tuhuma har guda 11, amma ta musanta aikata dukkan laifukan.
Sauran tuhume-tuhumen sun haɗa da rashawa, saɓa dokokin ƙasa da dokar sadarwa.
Idan an same ta da laifi, za a iya yanke ma ta hukuncin ɗaurin fiye da shekaru 100 a gidan yari.
A ranar Litinin, kotu ta ɗaure Win Myint, tsohon shugaban ƙasa kuma aminin Suu Kyi bisa tuhuma iri ɗaya.
A halin yanzu ba a san ko za a tura su gidan yari nan take bane ko kuma za a saurari shari’ar sauran tuhume-tuhumen da ake yi musu.